Mataimakin shugaban majalisar dokokin kasar Uzbekistan na farko, kana darektan hukumar kula da harkokin kare hakkin bil-adama, Akmal Saidov ya bayyana cewa, wasikar taya murna da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aikawa babban taron dandalin tattaunawa kan harkokin kare hakkin bil Adama na kasa da kasa, ta nuna cikakkiyar fahimta da tunaninsa kan aikin raya harkokin kare hakkin dan Adam.
Akmal Saidov ya bayyana haka ne a lokacin da yake halartar taron a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
A bana ake cika shekaru 30 da gabatar da sanarwar Vienna da shirin ayyuka. Wannan takarda ta gabatar da muhimman ka’idoji kamar haka, “ya kamata al’ummomin kasa da kasa su inganta hadin gwiwar kasa da kasa mai inganci, da tabbatar da ‘yancin samun bunkasuwa, da kawar da matsalolin ci gaba”, kuma ana daukarta a matsayin daya daga cikin muhimman takardu a tarihin ci gaban hakkin bil-adama a duniya.
Yau shekaru 30 bayan haka, duniya ta shiga wani sabon yanayi na tashin hankali da sauye-sauye.
A kan wannan batu, ina aikin kare hakkin bil-adama na duniya ya dosa?
A ranar 14 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da wasikar taya murna ga babban taron dandalin tattaunawa kan harkokin kare hakkin bil Adama na kasa da kasa, inda a cikinta ya ba da shawarar kare hakkin bil’adama ta hanyar tsaro, da inganta hakkin ta hanyar neman ci gaba, da ciyar da hakkin gaba ta hanyar hadin gwiwar al’ummun duniya, da aiwatar da shirye-shiryen tsaro na duniya, da ayyukan raya kasa, da daukaka matsayin wayewar kai a duniya.
Wannan ita ce shawara ta baya-bayan nan da kasar Sin ta gabatar kan yadda ake tafiyar da harkokin kare hakkin dan Adam a duniya, wadda ke da matukar muhimmanci, kuma ta ba da muhimman ka’idoji don inganta hadin gwiwar mabambantan kasashe kan kare hakkin bil-adama, wadda ta samu karbuwa sosai daga mahalarta taron nan da ke gudana a Beijing. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)