Bari mu siffanta duniyarmu a matsayin wani babban kauye, inda mazauna kauyen ke fuskantar matsalolin tsaro iri daban-daban. Wasu rikice-rikicen da aka dade ana fama da su, kamar su rikicin Rasha da Ukraine, da zaman dar-dar a yankin Gabas ta Tsakiya, suna kawo babban tsaiko ga zaman lafiyar kasa da kasa. Sai dai kuma sauran wasu matsaloli ko barazana da ba a saba ba, ciki har da matsanancin yanayi sakamakon sauyin yanayi, da matsalar yunwa sakamakon rashin isasshen abinci da ke addabar miliyoyin jama’a, da kuma barazanar hare-haren intanet ga muhimman ababen more rayuwar al’umma, duk suna damun jama’a sosai.
A irin yanayin da duniyarmu take ciki, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarar tabbatar da tsaro a duk fadin duniya a shekara ta 2022, shawarar da ta kunshi wasu muhimman ra’ayoyi hudu:
Na farko, tsayawa kan ra’ayin tabbatar da tsaro daga dukkan fannoni, wato ba bangaren soja kawai tsaro ya shafa ba, har ma akwai sauran bangarori da ke da alaka sosai ga harkar tsaro, ciki har da tattalin arziki, da hada-hadar kudi, da kiwon lafiya, da muhalli, da abinci, da kuma intanet.
Na biyu, nacewa ga bin ka’idar tabbatar da tsaro na bai daya, inda aka jaddada cewa, bai kamata wata kasa ta sadaukar da tsaron wata kasa ta daban, don kawai nemo wa kanta tsaron ba.
Na uku, ba da ra’ayin samun tsaro kafada da kafada, inda aka jaddada cewa, ya dace kasa da kasa su yi fatali da ra’ayin nuna wa juna fito-na-fito, kana, su fuskanci dimbin kalubalen tsaro cikin hadin-gwiwa.
Na hudu wato na karshe, tallata ra’ayin tabbatar da tsaro mai dorewa, wato a maida hankali kan dorewar tsaro na wani dogon lokaci. Alal misali, yayin da ake daidaita rikicin wani yanki, bai dace a dogara kan matakan soja kadai ba, ya kamata a nemo mafita tun daga asalin rikicin.
Wannan shawarar tsaron da shugaba Xi Jinping ya gabatar, ta samu amincewa sosai daga mutanen kasa da kasa, inda ya zuwa yanzu, ta riga ta samu goyon-baya daga kasashe da yankuna da kungiyoyin kasa da kasa fiye da 120, kana kuma, an rubuta shawarar cikin takardun hadin-gwiwa sama da 120 game da mu’amalar kasar Sin da sauran kasashe da kungiyoyin kasa da kasa.
Shawarar ta kuma shaida cewa, tsaro ba harka ce ta wata kasa ita kadai ba, harka ce da ke bukatar tafiya gaba cikin hadin-gwiwa. Kana kuma ko wace kasa za ta iya cin alfanu daga ciki. Kamar yadda masharhantan kasa da kasa suka bayyana, shawarar nan ta samar wa duniyarmu da ke fama da rikice-rikice wani abun da take matukar bukata, wato “kyakkyawan fata”. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp