Lagos, cibiyar tattalin arziki a Najeriya, kana daya daga cikin birane mafi yawan al’umma a yammacin Afrika, amma yana fama da cunkoson ababan hawa. Lokacin da na yi aiki a Najeriya, na kan je ziyarar aiki a Lagos, inda bayan na fita daga filin jirgin sama na kan shafe sa’o’i 5 a kan hanya, duk da cewa nisan bai kai kilomita 30 ba. Daga baya, wani abokina ya gaya min cewa, jirgin kasa da aka samar ya sassauta wannan hali da ake ciki a birni na Lagos, kwanan baya na kai ziyara Najeriya, har ma na je Lagos don ganewa idona wannan jirgin kasa.
Wannan layin dogo na jirgin kasa, shi ne irinsa na farko da wani kamfanin Sin ya tsara, ya gina tare da gudanarwa a yammacin Afirka,. Yana da tsawon kilomita 13 da tasoshi 5, kuma shi ne layin farko da ya ratsa yammacin Lagos. Yayin da na shiga wata tasha, na ga na’urar binciken tsaro ta zamani, da wurin sayar da tikiti, da ake sayarwa kan farashin Naira 700. Kuma taragun jirgin ya yi kama da wadanda ke kasar Sin. Na gamu da wani fasinja mai suna Adamu a tashar, ya gaya min cewa, wannan jirgi ya sassauta matsalar cunkuson ababan hawa a kan hanya a Lagos, a baya yana shafe sa’o’i 3 a babur mai kafa uku kafin ya isa wurin aikinsa, amma yanzu mintoci 15 kawai yake bukata, matakin da ya kyautata zaman rayuwarsa da ma inganta birnin. Ya ce, yana godiya matuka ga aikin da kamfanin Sin ya yi.
A cikin taragan an rataya tutar kasashen biyu, wanda ya alamanta hadin gwiwar kasashen biyu karkashin shawarar “ziri daya da hanya daya”. Jirgin dake zirga-zirga a birnin Lagos ba ma kawai ya kyautata zaman rayuwar al’ummar wurin ba, har ma ya ingiza bunkasuwar tattalin arzikin wannan yanki. Kazalika, ya zama daya daga ayyuka dake zama misalai na kyautata zaman rayuwar jama’a a Afrika karkashin shawarar “ziri daya da hanya daya”, wanda ya amfanawa al’ummar wurin. (Mai zana da rubuta: MINA)