Sakamakon yadda ake fuskantar karancin ruwan sama a jihar Borno, a wannan damina ta bana, Mai Martaba Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai Elkanemi, ya bukaci al’ummar musulmi a jihar da su fita rokon ruwa.
A don haka, Shehun Borno, ya bukaci al’ummar musulmi a jihar su fito kwansu da kwarkwata domin yin addu’o’in rokon ruwa ga Allah Madaukakin Sarki.
- Zulum Ya Kaddamar Da Kwalejin Ilimi Ta Farko A Jihar BornoÂ
- Musabbabin Haramta Sana’ar Gwangwan A Jihar Borno
Shehu ya sanar da hakan a wata sanarwar manema labaru mai dauke da sa-hannun Sakatarensa, Zannah Umar Ali, inda ya bayyana cewa za a gudanar da sallar rokon ruwan ta raka’a biyu, yau Litinin a filin kare gudunka na Ramat Square dake Maiduguri, da misalin karfe 10:00 na safiya.
Har wala yau, sanarwar ta bukaci al’ummar musulmi; maza da mata, yara da kanana tare da dattawa masu yawan shekaru don halartar sallar rokon ruwan, da neman taimakon Allah wajen samun ruwan sama.