• English
  • Business News
Friday, October 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sheikh Dahiru Bauchi Ya Bukaci A Gudanar Da Bincike Kan Kisan Masu Maulidi A Kaduna

by Khalid Idris Doya
2 years ago
Bauchi

Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya yi tir da Allah wadai da kisan da sojoji suka yi wa masu maulidi da cewa hakan kan ya faru ne bisa ‘kuskure’, inda ya misalta hakan da babban sakacin da bai kamata ya faru ba. 

Dahiru Bauchi a saƙon jajensa da ya aike wa musulman duniya kan kisan masu Maulidi kauyen Tudun Biri da ke ƙaramar hukumar Igabi a Kaduna da ake zargin mutum kusan 85 sun rasa rayukansu yayin da wasu sama da 50 suka jikkata a daren ranar Lahadi yayin da suke zaman tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad wato Maulidi.

  • Taron SGI Na Gudana Kan Sauyin Yanayi Karo Na 28
  • Gwamnan Gombe Ya Gabatar Da Naira Biliyan N207.75bn A Matsayin Kasafin 2024

Shehin ya bukaci gwamnati da ta gabbata kafa kwamitin bincike da zai gano waɗanda suka aikata hakan domin hukunta su.

A cewarsa, koda sojojin sama sun ce ba su da masaniya kan kisan, amma alhakin kula da yaƙi ta sama na wuyarsu don haka su ma akwai sakacinsu, ya kuma dora laifin ga sojojin sama da na kasa da kuma gwamnati.

Kazalika, babban malamin darikar ya nemi gwamnati ta biya diyyar masu maulidin da suka rasa rayukansu sakamakon ruwan bama-bamai da sojoji suka yi musu.

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Kama Motar Hilux Ɗin Da Aka Sace A Kano A Hanyar Zuwa Nijar

Jami’an Tsaro Sun Cafke Ɓarayin Kayayyakin Turakun Wutar Lantarki Na Hanyar Mando Zuwa Jos

A cewarsa: “Ina yin ta’aziyya ga dukkanin musuluman duniya da musulman Afrika da musulman Nijeriya a kan abun da ya faru, wanda ya faru a Kaduna mun bincika sun ce wai ba jiragen saman sojojin Nijeriya ba ne, sojojin kasan Nijeriya ko sun ce su ne, to ai su babu dama su hau sama. Saboda haka mun yi mamakin yadda aka rasa rayuka.”

Ya ce, babban mai laifi kan wannan lamarin ita ce gwamnati domin ita ce ta yi sake.

“Haƙiƙa mun ji zafi! mun ji zafi!! kuma muna yin ta’aziyya ga dukkanin musulmai na duniya bisa ga wannan rashin da muka yi.”

“Mun kuma yi mamakin yadda sojojin saman Nijeriya suka ce ba su san da harin ba, mun yi mamaki yadda suka hau soma suka sako bam kan mutane. Mun yi mamakin yadda aka kona kusan mutum dari. Wannan hakika ya yi yawa.”

Ya ce, wannan babban sake ne da ya kama tun daga kan sojojin sama domin a cewarsa su ne ke da alhakin kula da yaƙin sama, da su kansu sojojin kasan hadi da ganin laifin gwamnati kan harin da ya farun.

Ya yi kira ga gwamnati da ta gaggauta kafa kwamiti domin binciko ta yadda lamarin ya faru da har aka kashe mutane kusan 100.

“Muna neman su sanar da mu yadda aka ƙona mana masu maulidi a jirgin sama. Mun ji zafi matuka. Gwamnati tana nan tana kallo aka yi wannan abun a gabanta, don haka muna neman ta biya diyya na mutanenmu masu maulidi,” Sheikh Dahiru ya shaida.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

‘Yansanda Sun Kama Motar Hilux Ɗin Da Aka Sace A Kano A Hanyar Zuwa Nijar
Labarai

‘Yansanda Sun Kama Motar Hilux Ɗin Da Aka Sace A Kano A Hanyar Zuwa Nijar

October 9, 2025
TCN
Labarai

Jami’an Tsaro Sun Cafke Ɓarayin Kayayyakin Turakun Wutar Lantarki Na Hanyar Mando Zuwa Jos

October 9, 2025
Nijeriya Ta Yi Asarar Ganga Miliyan 13.5 Na Ɗanyen Mai Ta Hanyar Sata Da Zagon-ƙasa – NEITI
Labarai

Nijeriya Ta Yi Asarar Ganga Miliyan 13.5 Na Ɗanyen Mai Ta Hanyar Sata Da Zagon-ƙasa – NEITI

October 9, 2025
Next Post
Jami’in Diflomasiyyar Falasdinu: PA Ta Godewa Kasar Sin Bisa Aikewa Da Agaji Ga ’Yan Gaza Cikin Sa’o’in Bukata

Jami’in Diflomasiyyar Falasdinu: PA Ta Godewa Kasar Sin Bisa Aikewa Da Agaji Ga ’Yan Gaza Cikin Sa’o’in Bukata

LABARAI MASU NASABA

An Jinjinawa Tallafin Kamfanonin Sin Ga Tsarin Bunkasa Masana’antun Senegal

An Jinjinawa Tallafin Kamfanonin Sin Ga Tsarin Bunkasa Masana’antun Senegal

October 9, 2025
Masu Kallon Fina-Finai Na Sin Sun Gamsu Da Fina-Finan Da Aka Gabatar A Lokacin Hutun Bikin Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar Sin Ta 2025

Masu Kallon Fina-Finai Na Sin Sun Gamsu Da Fina-Finan Da Aka Gabatar A Lokacin Hutun Bikin Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar Sin Ta 2025

October 9, 2025
‘Yansanda Sun Kama Motar Hilux Ɗin Da Aka Sace A Kano A Hanyar Zuwa Nijar

‘Yansanda Sun Kama Motar Hilux Ɗin Da Aka Sace A Kano A Hanyar Zuwa Nijar

October 9, 2025
Sin Na Ci Gaba Da Goyon Bayan Kawo Karshen Rikicin Gaza

Sin Na Ci Gaba Da Goyon Bayan Kawo Karshen Rikicin Gaza

October 9, 2025
TCN

Jami’an Tsaro Sun Cafke Ɓarayin Kayayyakin Turakun Wutar Lantarki Na Hanyar Mando Zuwa Jos

October 9, 2025
An Yi Tafiye-tafiye Miliyan 16.34 Da Suka Shafi Shiga Da Fita Daga Kasar Sin Yayin Hutun Kwanaki 8 Na Kasar 

An Yi Tafiye-tafiye Miliyan 16.34 Da Suka Shafi Shiga Da Fita Daga Kasar Sin Yayin Hutun Kwanaki 8 Na Kasar 

October 9, 2025
Nijeriya Ta Yi Asarar Ganga Miliyan 13.5 Na Ɗanyen Mai Ta Hanyar Sata Da Zagon-ƙasa – NEITI

Nijeriya Ta Yi Asarar Ganga Miliyan 13.5 Na Ɗanyen Mai Ta Hanyar Sata Da Zagon-ƙasa – NEITI

October 9, 2025
Duniya Ta Kara Ganin Bunkasuwar Sin a Lokacin Hutun Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar

Duniya Ta Kara Ganin Bunkasuwar Sin a Lokacin Hutun Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar

October 9, 2025
Fursunoni Ba Za Su Samu Damar Kada Kuri’a Ba A Zaben 2023 – INEC

Batun Umarnin Kotu Na Kama Tsohon Shugaban INEC Ƙage Ne Kawai – Shugaban Jam’iyyar AA 

October 9, 2025
An Samu Karuwar Sayayya Yayin Hutun Bikin Kafuwar Kasar Sin

An Samu Karuwar Sayayya Yayin Hutun Bikin Kafuwar Kasar Sin

October 9, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.