Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, ya sake yin kira ga gwamnatin tarayya da ta tattaunawa da ‘yan bindiga a kokarin ganin an sako ‘yan Nijeriya da ke tsare a maboyarsu.
In ba a manta ba, Shehin Malamin a lokacin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi kira ga gwamnati da ta dinga tattaunawa da ‘yan bindiga a wani yunkuri na shawo kan kalubalen ta’addancinsu.
- Gobara Ta Hallaka Yara 2 A Sansanin ‘Yan Gudun Hijira A Borno
- NEDC Ta Rarraba Kayayyakin Noman Rani A Jihar Yobe
A cikin wata sanarwa da ya fitar, malamin ya ce, a shirye yake ya shiga tsakani don samar da cikakkiyar tattaunawa tsakanin gwamnatin tarayya da ‘yan bindiga.
Sheikh Gumi ya nemi shugaba Tinubu da cewa, kada ya sake maimaita kuskuren da Buhari ya yi inda ya ki amincewa da bude hanyar tattaunawa.
Malamin ya yi kiran ne yayin da yake tofa albarkacin bakinsa kan kin amincewa da gwamnatin jihar Kaduna ta yi na tattaunawa da ‘yan bindigar da suka yi garkuwa da dalibai 287 na Sakandaren gwamnatin Kuriga da kuma firamare a karamar hukumar Chikun a makon da ya gabata.
Shehin Malamin ya ce, kin amincewa da tattaunawa ba matakin daidai ba ne da ya kamata a dauka.