• English
  • Business News
Thursday, November 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shekaru 25 Da Dawowar Macao: Nasarori Da Hangen Gaba

by CGTN Hausa and Sulaiman
11 months ago
Macao

LABARAI MASU NASABA

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

Rubu’in karni ke nan da dawowar Macao cikin kasarsa ta asali, hakan ya kasance wani muhimmin ci gaba a cikin babbar tafiyar farfado da al’ummar kasar Sin. Tun daga wannan lokacin, ta hanyar bin manufar “kasa daya, tsarin mulki biyu”, Macao ya samu sauyi mai ban mamaki, godiya ga nasarorin da aka samu a sassa daban-daban, kama daga bangaren siyasa, tattalin arziki da zamantakewa zuwa al’adu. A gun taron murnar zagayowar wannan rana da bikin kaddamar da wa’adi na shida na gwamnatin yankin musamman na Macao a ranar 20 ga watan Disamba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yaba da wadannan nasarori da aka samu, kuma ya bayyana babbar fata ga wannan yankin na musamman na kasar Sin, ta mahangar ci gaban kasa.

Tun bayan dawowarsa, Macao ya samu karuwar tattalin arziki mai matukar daukar hankali. Alal misali, a rabin farko na shekarar 2024, GDPn Macao ya kai kusan biliyan 204 na kudin Macao wato MOP, kusan dala biliyan 25.5. Yayin da a shekara 1999, kafin dawowar, GDPn ya kasance MOP biliyan 51.9, kimanin dala biliyan 6.48. Har ila yau, kafin 1999, Macao yana da karancin albarkatun ilimi, mazauna kalilan ne ke zuwa jami’a. A yau, jimillar yawan shigar daliban yankin manyan makarantu ya haura kashi 95 cikin dari. Kana yawan jami’o’i a Macao ya karu daga jami’a guda zuwa 10, wadanda ke taka muhimmiyar rawa wajen raya tarin hazaka masu muhimmanci don ci gaban Macao. Hakazalika, shugaba Xi ya yaba wa tsarin mulkin da ya shafi jama’ar Macao, inda ya bayyana irin ci gaban da aka samu a fannin ayyukan yi, da gidaje, da ilimi, da kiwon lafiya, da tsaro, da sauran shirye-shiryen zamantakewar al’umma. Wannan cikakkiyar hanya ta haifar da zaman lafiya da kwanciyar hankali na dogon lokaci.

Dangane da hangen gaba kuwa, Macao zai ci gaba da sa kaimi ga kara kyautata mu’amala tsakaninta da mazauna yankin a bangaren kiyaye ka’idoji da dokoki, da jagorantar ci gaban kungiyoyi, da inganta tushen ginshikin gudanar da tsarin mulki, ta hanyar kara inganta tsarin da ya shafi jama’a, da gaggauta magance matsaloli da suka shafi jama’a, da samar da yanayi mai kyau na zamantakewa, da kuma tabbatar da burin mazauna yankin na samun ingantacciyar rayuwa. Bugu da kari, zai ci gaba da inganta damammaki ga duk ma’aikata masu basira, da mayar da hankali kan magance bukatun matasa, da samar da daidaito na zamantakewa, adalci, jituwa, da kwanciyar hankali. (Mohammed Yahaya)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki
Daga Birnin Sin

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka
Daga Birnin Sin

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

November 5, 2025
Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

November 5, 2025
Next Post
Saka Zai Yi Jinyar Makonni Bayan Raunin Da Ya Samu

Saka Zai Yi Jinyar Makonni Bayan Raunin Da Ya Samu

LABARAI MASU NASABA

Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata

Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata

November 6, 2025
Gwamnatin Tinubu “Kasuwa Ce Mara Amfani Ga Talaka” – PDP

Majalisa Ta Ɗage Tantance Ministan Tinubu Saboda Rashin Rahoton Tsaro

November 6, 2025
Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

November 5, 2025
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

November 5, 2025
Majalisar Dattawa

Majalisa Ta Amince Da Ɗaurin Shekaru 14 A Gidan Yari Ga Malamai Masu Cin Zarafin Mata A Jami’o’i

November 5, 2025
Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

November 5, 2025
Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

November 5, 2025
Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

November 5, 2025
Gwamna Yusuf

Malam Triump: Ƙungiyoyin Ɗariƙun Sufaye Sun Maka Gwamnan Kano A Kotu

November 5, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.