Kasar Sin ta harba kumbon Shenzhou-20 a yau Alhamis, inda ta aike da ‘yan sama-jannati 3 zuwa tashar sararin samaniyar kasar domin gudanar da aikin bincike na tsawon watanni shida.
An harba kumbon ne da misalin karfe 5:17 na maraice agogon Beijing, watau karfe 9:17 na safiya agogon GMT, daga cibiyar harba tauraron dan’adam ta Jiuquan da ke arewa maso yammacin kasar Sin, a cikin wani roka samfurin Long March-2F. Kumbon ya rabu da rokar tare da shiga cikin da’irar sararin samaniyar da ake so bayan mintuna 10 da harbawa.
- Shugaba Xi Ya Jaddada Aniyar Kasarsa Ta Goyon Bayan Kudurorin Kyautata Yanayi Da Ci Gaba Marar Gurbata Muhalli
- Tallafa Wa Al’umma: Ya Dace Gwamnoni Su Yi Koyi Da Jihar Zamfara – UNDP
Hukumar kula da sararin samaniya ta kasar Sin (CMSA) ta bayyana cewa, ‘yan sama-jannatin na kasar Sin, ko kuma ‘taikonauts’ kamar yadda ake musu lakabi, da ke cikin kumbon suna cikin kyakkyawan yanayi tare da koshin lafiya.
Sabbin ‘yan sama-jannatin da aka tura, za su gudanar da gwaje-gwaje da bincike game da yanayin rayuwa a sararin samaniya, da kimiyyar karamar fizgar kasa ko jazibiyya (micro-gravity physics) da sabbin fasahohin sararin samaniya.
Kazalika, za su kuma yi tafiye-tafiye mabambanta a sararin samaniya don kakkafa shingayen kariya daga baraguzai da tarkacen sararin samaniya, da kuma girkewa da dawo da na’urorin da aka makala a wajen tashar.
Ya zuwa yanzu dai, ‘yan sama jannatin kasar Sin 26 ne suka yi nasarar zuwa sararin samaniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere).