Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya jaddada kudirin gwamnatin tarayya na ci gaba da farfado da tattalin arzikin yankin Arewa maso Gabashin ƙasar nan.
Ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da ginin hedikwatar hukumar raya Arewa maso Gabas (NEDC) a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.
- Hajjin Bana: Zafi Ya Yi Ajalin Alhazai Sama Da 900 A Saudiyya
- Kamata Ya Yi NATO Ta Daina Hura Wutar Rikicin Rasha Da Ukraine
Ya ce aikin wani mataki ne na cika alkawarin da shugaba Tinubu ya yi na bayae da fifikon ayyukan da za su kare muradun jama’ar yankin Arewa maso Gabas.
Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma duba yadda aikin kashin farko na hanyar Jere Bowl mai tsawon kilomita 27 a karamar hukumar Mafa/Jere, ke gudana.
Gwamnan Gombe Muhammad Inuwa Yahaya, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar gwamnonin jihohin Arewa, ya yaba wa Shettima, bisa yadda ya bayar da muhimmanci wajen gudanar da ayyukan hukumar ta NEDC.
Ya yi kira ga sauran masu ruwa da tsaki daga jihohin Arewa maso Gabas, da su kara kaimi wajen ganin an samu nasarar gudanar da ayyukan bisa manufofin NEDC.
Shugaban Hukumar Gudanarwar Hukumar NEDC, Manjo Janar Paul Tarfa (mai ritaya), ya ce dasa tubalin ginin hedikwatar ya bude sabon babi a tarihin hukumar, wanda ke nuna ci gaba.
A ɗayan ɓangaren, kuma makamancin haka, mataimakin shugaban kasar ya kaddamar da rabon kayan amfanin gona domin haɓaka harkar noma a yankin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp