Shugaba Bola Tinubu ya bayyana matukar alhininsa ga al’ummar Nijeriya dangane da rasuwar Hajiya Binta (Dada) ‘Yar’aduwa, mahaifiyar marigayi shugaban kasa Umaru Musa ‘Yar’aduwa da tsohon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya, marigayi Janar Shehu Yar’adua.
Yayin da al’ummar kasar ke cike da alhinin rasuwarta, Shugaban kasar ya ce rasuwar Hajiya ‘Yar’aduwa, wadda ta rasu a daren ranar Litinin, rashi ne ba kawai ga dangi ko Jihar Katsina kadai ba, rashi ne ga al’ummar kasa baki daya.
- Za A Nuna Shirin Talabijin Na Gaskiya Mai Taken “Ciyawar Kasar Sin” A Tashar CCTV-4
- Ƴan Sakkwato Sun Yi Murnar Komawar Ministan Tsaro Don Kawo Ƙarshen Ƴan Ta’adda
Shugaban ya bayyana haka ne a ranar Talata ta bakin mataimakinsa, Kashim Shettima, wanda ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya wajen jana’izar marigayiya Hajiya Binta (Dada) ‘Yar’aduwa a jihar Katsina.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa a ofishin mataimakin shugaban kasa, Stanley Nkwocha, ya fitar, shugaba Tinubu ya yabawa marigayiyar, inda ya kwatanta ta a matsayin uwa kuma Adon garin mata.