A watan Nuwamban ko wace shekara, Mark Bacon kan tuna da labarin da ke tsakaninsa da shugaban kasar Sin Xi Jinping. A ranar 25 ga watan Nuwamban shekarar 2023, ya wallafa wani sako a shafin manhajar sada zumunta, inda ya ce, “A ranar 18 ga watan Nuwamban shekarar 2014, na yi sa’a sosai da na samu damar haduwa da shugaba Xi Jinping da uwargidansa, bayan sun isa birnin Hobart, sa’an nan mun yi hira har na tsawon fiye da awa guda”.
Yayin da Shugaba Xi ya yi ziyarar aiki a kasar Australiya a shekarar 2014, ya gana da Mark Bacon da iyalinsa.
- OECD: Gdpn Sin Zai Karu Da Kashi 5.2 A 2023
- Labarin Zamanintarwa Irin Na Kasar Sin: Kimiyya Na Taimakawa Manoma Fita Daga Kangin Talauci
A shekarar 1999 da ta 2001, Jim Bacon, mahaifin Mark Bacon ya ziyarci lardin Fujian na kasar Sin har sau biyu a matsayinsa na gwamnan jihar Tasmania, kuma ya samu tarba daga wajen Xi Jinping, wanda yake aiki a lardin a wancan lokaci.
Bayan komawarsa gida, yayin da yake ambato Xi Jinping, gwamna Jim Bacon ya gaya wa dansa Mark Bacon da iyalinsa cewar, “Ya fi kyau ku rika tunawa da sunansa, shi ne wanda zai kula da babban aiki.”
Gwamna Jim Bacon shi ma ya taba gayyatar Xi Jinping wanda ke rike da mukamin shugaban lardin Fujian a wancan lokaci don ziyartar jihar Tasmania, amma abin bakin ciki shi ne, ba su sake haduwa ba sakamakon rasuwar gwamna Jim Bacon a shekarar 2004.
A ranar 18 ga watan Nuwamban shekarar 2014, Xi Jinping, a matsayinsa na shugaban kasar Sin ya ketare babban teku don cimma burin wannan haduwa.
Mark Bacon ya bayyana cewa, “ya nuna girmamawa ga mahafina wanda ya riga mu gidan gaskiya, muna matukar godiya. Sau da dama ya karfafa min gwiwa wajen ziyartar lardin Fujian, kana mun tattauna kan labaran Sin da Australiya, da farfadowar kasar Sin, da saurin ci gaban tattalin arzikinta, da ma babbar ma’anar da wadannan ci gaba ke kawowa al’ummar Sinawa, musamman ma masu fama da talauci.”(Kande Gao)