• English
  • Business News
Thursday, October 23, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shin Kasar Amurka Za Ta Iya Cika Alkawarinta?

by CMG Hausa
3 years ago
Kasar Amurka

Kwanan baya, kasar Amurka ta kira taro karo na 2 na shugabanninta da na kasashen Afirka, shekaru 8 bayan shirya taron a karon farko.

Idan aka kalli tsarin taron, za a ce wani gagarumin biki ne, wanda ya samu halartar shugabannin kasashe 49 dake nahiyar Afirka, da na kungiyar tarayyar Afirka AU, gami da takwarorinsu na kasar Amurka.

  • Shugaban Kasar Sin Ya Tattauna Da Takwaransa Na Cote d’Ivoire

A cewar fadar White House, ta wannan taro, kasar Amurka ta kuduri aniyyar zurfafa huldarta da nahiyar Afirka, kana gwamnatin kasar karkashin jagorancin shugaba Joe Biden ta sanar da shirin zuba jari na dala biliyan 55 ga kasashen Afirka, cikin shekaru 3 masu zuwa.

Duk da haka, ba a rasa ce-ce-ku-ce game da taron. Misali, tsohuwar jakadiyar kungiyar AU a kasar Amurka , Arikana Chihombori-Quao, ta ce taron ba zai haifar da da mai ido ba, illa dai Amurkawa su ci gaba da nuna bambanci ga jama’ar nahiyar Afirka.

Hakika kasashen Afirka na da dimbin al’umma da albarkatun kasa, inda tattalin arzikinsu ke sauyawa daga na salon gargajiya zuwa irin na zamani, don haka suna bukatar samun karin jari daga kasashen ketare, wanda zai iya taimakawa kokarinsu na raya kasa. Sai dai a ganin wasu masana masu nazarin al’amuran kasa da kasa, dalilin da ya sa kasar Amurka ke son kara zuba jari a nahiyar Afirka, shi ne domin neman biyan bukatarta ta samun fifiko yayin takara da sauran kasashe.

LABARAI MASU NASABA

Diflomasiyyar Shugabanni Na Matukar Taka Rawar Gani Wajen Jagorantar Dangantakar Sin Da Amurka

Yawan Hada-hadar Kudaden Kasashen Waje Na Kasar Sin A Farkon Rabu’i Na Uku Na Bana Ya Zarce Dala Triliyan 11

Abun da kasashen Afirka suke bukata, shi ne taimakon da aka bayar bisa sahihanci. Idan kasar Amurka na son daidaita huldarta da kasashen Afirka, to, ya kamata ta girmama kasashen Afirka, da samar musu da hakikanan abubuwa masu amfani da suke bukata, yayin da suke kokarin raya tattalin arzikinsu. (Bello Wang)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kungiyar IOMed Za Ta Taka Rawar Gani Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya 
Daga Birnin Sin

Diflomasiyyar Shugabanni Na Matukar Taka Rawar Gani Wajen Jagorantar Dangantakar Sin Da Amurka

October 22, 2025
Yawan Hada-hadar Kudaden Kasashen Waje Na Kasar Sin A Farkon Rabu’i Na Uku Na Bana Ya Zarce Dala Triliyan 11
Daga Birnin Sin

Yawan Hada-hadar Kudaden Kasashen Waje Na Kasar Sin A Farkon Rabu’i Na Uku Na Bana Ya Zarce Dala Triliyan 11

October 22, 2025
Nesa Ta Zo Kusa: Maraba Da Sabon Jirgin Kasa Samfurin CR450 Da Kasar Sin Ta Kera
Daga Birnin Sin

Nesa Ta Zo Kusa: Maraba Da Sabon Jirgin Kasa Samfurin CR450 Da Kasar Sin Ta Kera

October 22, 2025
Next Post
Na Fara Shirye-Shiryen Hada Kayana Don Komawa Daura Nan Da Watanni Biyar 5 —Buhari

Na Fara Shirye-Shiryen Hada Kayana Don Komawa Daura Nan Da Watanni Biyar 5 —Buhari

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Abba Ya Jaddada Mubaya’arsa Ga Kwankwaso 

Gwamna Abba Ya Jaddada Mubaya’arsa Ga Kwankwaso 

October 23, 2025
Shugabannin jam’iyyar PDP Na Arewa Sun Amince Da Turaki A Matsayin Ɗan Takarar Shugabancin Jam’iyyar Na Ƙasa

Shugabannin jam’iyyar PDP Na Arewa Sun Amince Da Turaki A Matsayin Ɗan Takarar Shugabancin Jam’iyyar Na Ƙasa

October 23, 2025
Yajin aiki

Gwamnatin Tarayya Ta Jajantawa Waɗanda Fashewar Tankar Mai Ta Rutsa Da Su A Neja 

October 23, 2025
Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Naira Biliyan 2.5 Na Aikin Haƙo Uranium, Mai Da Iskar Gas

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Naira Biliyan 2.5 Na Aikin Haƙo Uranium, Mai Da Iskar Gas

October 23, 2025
Kungiyar IOMed Za Ta Taka Rawar Gani Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya 

Diflomasiyyar Shugabanni Na Matukar Taka Rawar Gani Wajen Jagorantar Dangantakar Sin Da Amurka

October 22, 2025
NUJ Reshen Kano Ta Taya Ahmed Mu’azu Murna Kan Naɗin Da NAHCON Ta Yi Masa

NUJ Reshen Kano Ta Taya Ahmed Mu’azu Murna Kan Naɗin Da NAHCON Ta Yi Masa

October 23, 2025
Yawan Hada-hadar Kudaden Kasashen Waje Na Kasar Sin A Farkon Rabu’i Na Uku Na Bana Ya Zarce Dala Triliyan 11

Yawan Hada-hadar Kudaden Kasashen Waje Na Kasar Sin A Farkon Rabu’i Na Uku Na Bana Ya Zarce Dala Triliyan 11

October 22, 2025
Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

‘Yansanda Sun Cafke Wani Matashi Ɗan Shekara 15 Da Ake Zargi Da Yin Fashi Da Makami A Gombe

October 22, 2025
Nesa Ta Zo Kusa: Maraba Da Sabon Jirgin Kasa Samfurin CR450 Da Kasar Sin Ta Kera

Nesa Ta Zo Kusa: Maraba Da Sabon Jirgin Kasa Samfurin CR450 Da Kasar Sin Ta Kera

October 22, 2025
An Sake Saka Sunan Osimhen A Cikin ‘Yan Takarar Kyautar Gwarzon Dan Wasan CAF Na Bana

An Sake Saka Sunan Osimhen A Cikin ‘Yan Takarar Kyautar Gwarzon Dan Wasan CAF Na Bana

October 22, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.