Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirin ta na ba da goyon baya ga samar da wani shirin fim mai nuna tarihin shekaru 25 na dimokuradiyyar Nijeriya, bayanin hakan ya fito ne daga bakin Ministan Yada Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin Majalisar Tuntuba ta Jam’iyyun Siyasa, wato Inter-Party Adbisory Council (IPAC), a ranar Juma’ar da ta gabata a Abuja.
Ministan ya bayyana fim din, wanda IPAC ce ta yi tunanin a shirya shi, a matsayin muhimmin tarihin tafiyar da dimokiradiyyar Nijeriya yayin da kasar ke cika shekaru 25 a kan turbar mulkin na mutane, domin mutane kuma daga mutane.
- Trump Ya Bayyana Dalilin Rufe Gidan Rediyon Muryar Amurka
- Ranar Mata Ta Duniya: NPA Ta Mayar Da Hankali Wajen Kare ‘Yancin Mata –Dantsoho
Alhaji Muhammad Idris ya ce fim din tarihin zai nuna nasara, kalubale, da darussan da aka koya a wannan tafiya, ya ce “Na yi farin cikin ganin kokarin da IPAC da shugabanninta suke yi wajen karfafa dimokiradiyya, musamman ta hanyar fim din wanda zai zama wata muhimmiyar shaida ta tarihi, domin girmama jajirtattun yan siyasar kasarmu da kuma nuna jajircewar Nijeriya a harkar dimokiradiyya.
A kan haka, Gwamnatin Tarayya, ta hannun Ma’aikatar Yada Labarai da Wayar da Kai, za ta goyi bayan shirya wannan fim na musamman, ya kuma jinjina wa IPAC kan jajircewar ta wajen ci gaban dimokiradiyyar Nijeriya tare da jaddada muhimmancin hadin kan jam’iyyun siyasa bayan zabe domin karfafa hadin kan kasa da kawo ci gaba.
Gwamnatin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu tana goyon bayan a yi gasa mai kyau a siyasa, domin dimokiradiyya ta na bunkasa ne kawai idan ana samun hamayya mai ma’ana da hadin kai bisa muradin kasa ba tare da la’akari da bambancin jam’iyyun siyasa ba,” in ji Idris.
Ya kuma kara da cewa dorewar tsarin dimokiradiyya na bukatar hadin gwiwa daga kowane bangare, “Jam’iyyun siyasa su ne ginshikin dorewar dimokiraɗiyya, kuma yayin da hamayya take da muhimmanci a lokacin zabe, dole ne mu hada kai wajen gina kasar mu, hakan ya sa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, wanda babban jami’in dimokiradiyya ne yake mutunta gasa mai tsafta, amma kuma ya na fifita hadin kai da ci gaban kasa fiye da komai.
Shugaban IPAC na kasa, Honourable Yusuf Dantalle, ya ce shirin fim din na tarihi zai bayyana ci gaban da aka samu a fannonin gina ababen more rayuwa, kiwon lafiya, ilimi, da hadin kan al’umma, ya kuma ci gaba da “Fim din zai zama wani muhimmin tarihin kasa, zai kuma mayar da hankali kan matasa, musamman ‘yan zamani (Gen Z), domin ya zama wata hanyar ilmantarwa da hade kan ‘yan kasa domin su kara sanin abinda ake nufi da Dimokuradiyya a Nijeriya.
Fim din zai kunshi fitattun jaruman Nollywood kuma za a shirya shi da na’urori na zamani domin ya dace da matakin inganci na duniya, ta yadda babu wani wanda zai kalla ba tare da ya yaba wa wadanda su ka dauki nauyin shirya wannan kasaitaccen shiri.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp