Bayan da babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) ya watsa shirye-shiryen murnar bikin bazara na gargajiyar kasar Sin kai tsaye a wasu wuraren zaman jama’a dake birnin Nairobi, hedkwatar kasar Kenya dake gabashin Afirka, shirin fim na tallata shagalin murnar bikin kunna fitilu na gargajiyar kasar Sin, shi ma ya sauka a nahiyar Afirka, wanda ya jawo hankalin galibin jama’ar Afirka da Sinawa dake nahiyar.
A ranar 4 ga watan Fabrairu, wato ranar jajiberin bikin kunna fitilu, an watsa shirin fim na tallata shirin bikin kunna fitilu da CMG ya tsara a duk tsawon ranar a manyan alluna 7 dake babban yankin kasuwanci na Nairobi, da alluna 142 dake wasu yankunan kasuwanci da wuraren zaman al’umma, wanda ya jawo hankalin jama’ar Kenya da yawa, inda suka tsaya suka kalla, kuma dukkansu sun bayyana cewa, al’adun kasar Sin na da ban sha’awa da kuzari, kuma shirin da aka nuna ya zama zakaran gwajin dafi a fannin more al’adun Sinawa a wuraren taruwar jama’a dake birnin Nairobi.
Har ila yau, an kuma gabatar da shirin fim na tallata bikin kunna fitilu na gargajiya na kasar Sin, a dandalin taro na Nelson Mandela dake kasar Afirka ta Kudu, da kuma dandalin Meskel na kasar Habasha.
Ban da watsa shirin fim din ta hanyar alluna, Gidan Rediyon 5FM na Zambiya, da Kamfanin Watsa Labarai na Kenya, da kafar labarai ta Gleamer News dake Najeriya, da sauran manyan kafafen yada labarai na Afirka, sun yayata, tare da bayar da rahoto kan abubuwa da suke da nasaba da bikin kunna fitilu da CMGn ya tsara, wanda ya shafi mutane sama da miliyan 300. (Mai fassara: Bilkisu Xin)