Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata ya tashi daga birnin tarayyar Nijeriya zuwa Madrid da ke kasar Spain domin amsa gayyatar ziyarar aiki da shugaban Spanish, Pedro Sanched ya tura masa.
A cewar wata sanarwar da Kakakin Shugaban Kasa, Femi Adesina ya fitar, ya ce, a ziyarar, shugaban zai gana da manyan Kasar daban-daban, ciki har da ganawa da Sarki Felipe VI.
A cewar sanarwar, Shugabannin kasashen biyu za su tattauna muhimman batutuwa da suka shafi cigaban kasar su da ake sa ran zai kai ga cimma wata yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da zai kai ga kara inganta kyakkyawar alaka a tsakanin kasashen biyu.
Daga cikin bangarorin da za su Sanya hannun sun hada da musayar wadanda aka yanke wa hukunci bisa wani laifi, Harkokin da suka shafi al’adu, hadin kai wajen yaki da ta’addanci, tare da batutuwan da suka shafi lamuran diflomasiyya, zuba jari da kasuwanci, sufuri, kiwon lafiya da bunkasa harkokin wasanni.
Sannan, Buhari zai kasance babban bako a taron kungiyar kasuwanci kuma zai yi magana da wasu jami’an kasar Spanish kan harkokin da suka shafi bunkasa kasuwanci da masana’antu.
Jami’an da suka mara wa Buhari baya a wannan ziyarar sun hada da ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama; ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN); ministan kasuwanci da masana’antu, Otunba Adeniyi Adebayo; ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed; ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola; ministan wasanni da matasa, Sunday Dare; da kuma karamin ministan lafiya, Olorunnimbe Mamora.
Saura sun hada da: Mai baiwa Shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Maj-Gen Babagana Monguno (rtd); daraktan hukumar (NIA), Amb. Ahmed Rufa’i Abubakar; da shugaban hukumar kula da harkokin mazauna kasashen waje (NiDCOM), Hon. Abike Dabiri-Erewa.
Ana sa ran shugaba Buhari zai dawo Nijeriya a ranar Juma’a 3 ga watan June.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp