• English
  • Business News
Wednesday, October 29, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shugaba Tinubu Ya Dawo Abuja Daga Qatar

by Sulaiman
2 years ago
Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya sauka Abuja bayan ziyarar aiki ta kwanaki biyu da ya kai a ƙasar Ƙatar.

Jirgin shugaban ƙasa, mai lamba NAF 001, ya sauka a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da misalin ƙarfe 7 na dare.

  • Nijeriya Da Qatar Sun Rattaba Hannu Kan Yarjeniyoyi Daban-Daban
  • Ramadan: Sanata Abdulaziz Yari Zai Raba Tirela 358 Na Kayan Abinci A Jihar Zamfara

Tinubu ya kammala ziyararsa zuwa ƙasashen waje karo na 12 tun bayan da ya karɓi ragamar shugabancin ƙasar watanni tara da suka gabata, kuma ya yi kwana 75 a ƙasashen waje.

Tinubu ya samu tarba daga manyan jami’an gwamnati da suka haɗa da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima; Shugaban Ma’aikatan sa, Femi Gbajabiamila; Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume; Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike; Shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Ganduje; da Darakta Janar na Hukumar Tsaro, Yusuf Bichi, da dai sauran su.

A ranar farko ta ziyarar tasa, shugaban na Nijeriya ya ziyarci gidan adana kayan tarihi na Ƙatar inda ya jaddada muhimmancin rubuta sahihin bayanan tarihin ƙasa, da al’adu, da cigaba, da ƙalubale.

LABARAI MASU NASABA

DSS Ta Kama Wani Matashi Da Ya Yi Kira A Yi Juyin Mulki A Kafofin Sada Zumunta

An Kashe Ɗan Sanda Da Ɗan Hakimi A Rikicin Manoma Da Makiyaya A Gombe

Da yake rangaɗin jibgegen ginin wanda ya kai murabba’in mita 39,994 da ke kewaye da asalin fadar Sheikh Abdullah bin Jassim Al-Thani, shugaban ya ce, “Yana da kyau a rubuta al’adu tun farkon tarihi, al’adun wayewa, haɗin gwiwa, ƙalubale da jajircewar shugabanci.”

Washegari, Tinubu tare da Sarkin Ƙatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani sun shaida rattaba hannu kan wasu muhimman yarjejeniyoyi guda bakwai a tsakanin ƙasashen biyu, bayan ganawar sirri da suka yi a fadar shugaban ƙasa dake Doha.

Sun haɗa da: yarjejeniyar haɗin gwiwa a fagen ilimi; sanya ƙa’idojin ɗaukar ma’aikata tare da gwamnatin Ƙatar; kafa majalisar hada-hadar kasuwanci tsakanin Ƙungiyar ‘Yan Kasuwa da Masana’antu ta Ƙatar da Ƙungiyar ‘Yan Kasuwa da Masana’antu da Ma’adinai da Noma ta Najeriya; baya ga yarjejeniyar haɗin gwiwa a fagen matasa da wasanni.

Sauran yarjejeniyoyin sun haɗa da haɗin gwiwa a fannin yawon buɗe ido da harkokin kasuwanci, da kuma yarjejeniyar fahimtar juna da ke yaƙi da haramtacciyar fataucin miyagun ƙwayoyi.

Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, da jami’an gwamnatin Ƙatar, Buthaina bint Ali Al Jabr Al Nuaimi, Ministar Ilimi da Ilimi Mai Zurfi; Dr. Ahmad Hassen Al-Hammadi, Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Waje; Sheikh Khalifa Bin Jassim Al Thani, Shugaban Cibiyar Kasuwanci da Masana’antu ta Ƙatar da Abdullah bin Khalaf bin Hattab Al Kaabi, Mataimakin Sakatare na Ma’aikatar Cikin Gida ne suka sanya hannu kan takardun.

A ranar Lahadi ne Tinubu ya jagoranci Taron Kasuwanci da Saka Hannun Jari na Najeriya da Ƙatar inda ya buƙaci shugabannin masana’antu na Ƙatar da su kai rahoton duk wani jami’in Najeriya da ya nemi cin hanci kafin a bar su su yi kasuwanci a ƙasar.

Ya nanata cewa Najeriya ba zai ƙi cigaba ba saboda abubuwan da suka faru a baya da ke cike da jinkiri na gwamnati da cin hanci da rashawa da ke daƙile sauƙin kasuwanci.

“Kada ku ba da cin hanci ga kowa daga cikin jama’armu. Za ku sami damar zuwa gare ni, ” inji Tinubu.

Shugaban ya kuma tabbatar wa da ‘yan kasuwar duniya cewa Nijeriya a shirye take ta gudanar da harkokin kasuwanci da gaske domin gwamnatin sa za ta yi maganin duk wata maslaha a ƙasar da ke kawo cikas ga masu zuba jari a tattalin arziƙin Najeriya.

Ya kuma yi alƙawarin kawar da duk wasu matsaloli da ke kawo cikas ga harkokin kasuwanci yana mai cewa, “Kada ku bari hasashe ya zama cikas ga shirin ku na saka hannun jari. Nijeriya da gaske take game da kawo sauyi a fannin zuba jari.”

Ƙatar dai ita ce ƙasa ta uku a yankin Gulf da Tinubu ya kai ziyara tun bayan da ya ɗare kujerar shugabancin ƙasar da kuma ziyarar sa ta 16 a ƙasashen waje.

Ya zuwa yanzu, ya ziyarci birnin Paris na ƙasar Faransa (sau uku); Landan, Birtaniya; Bissau, Guinea-Bissau (sau biyu); Nairobi, Kenya; Porto Norvo, Jamhuriyar Benin; New Delhi, Indiya; Abu Dhabi da Dubai a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa; New York, Amurka, Riyadh, Saudi Arabia, Berlin, Jamus da Addis Ababa, Habasha.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwamnatin Rikon Kwarya: Shirin DSS Ne Na Damke Atiku Da Peter Obi Kafin Rantsar Da Tinubu
Labarai

DSS Ta Kama Wani Matashi Da Ya Yi Kira A Yi Juyin Mulki A Kafofin Sada Zumunta

October 29, 2025
An Kashe Ɗan Sanda Da Ɗan Hakimi A Rikicin Manoma Da Makiyaya A Gombe
Labarai

An Kashe Ɗan Sanda Da Ɗan Hakimi A Rikicin Manoma Da Makiyaya A Gombe

October 29, 2025
Ribadu Ya Gargaɗi ‘Yan Siyasa Kan Tayar Da Hankali A Zaɓen Anambra
Labarai

Ribadu Ya Gargaɗi ‘Yan Siyasa Kan Tayar Da Hankali A Zaɓen Anambra

October 29, 2025
Next Post
Birnin Beijing Na Shirin Samar Da Karin Masana’antu Da Wuraren Kere-kere Masu Amfani Da Fasahohin Zamani 100

Birnin Beijing Na Shirin Samar Da Karin Masana’antu Da Wuraren Kere-kere Masu Amfani Da Fasahohin Zamani 100

LABARAI MASU NASABA

Xi Jinping Zai Gana Da Donald Trump

Xi Jinping Zai Gana Da Donald Trump

October 29, 2025
Gwamnatin Rikon Kwarya: Shirin DSS Ne Na Damke Atiku Da Peter Obi Kafin Rantsar Da Tinubu

DSS Ta Kama Wani Matashi Da Ya Yi Kira A Yi Juyin Mulki A Kafofin Sada Zumunta

October 29, 2025
An Kashe Ɗan Sanda Da Ɗan Hakimi A Rikicin Manoma Da Makiyaya A Gombe

An Kashe Ɗan Sanda Da Ɗan Hakimi A Rikicin Manoma Da Makiyaya A Gombe

October 29, 2025
Ribadu Ya Gargaɗi ‘Yan Siyasa Kan Tayar Da Hankali A Zaɓen Anambra

Ribadu Ya Gargaɗi ‘Yan Siyasa Kan Tayar Da Hankali A Zaɓen Anambra

October 29, 2025
ADC Ta Gargaɗi Gwamnatin Tarayya Kan Amfani da Zargin Juyin Mulki Wajen Yaƙar ‘Yan Adawa

Ba Matakan Tinubu Ne Suka Karyar Da Farashin Kayan Abinci Ba – ADC

October 29, 2025
‘Yan Ta’adda Sun Yi Barazanar Sanya Wa Majalisa Bam – Ɗan Majalisa

‘Yan Ta’adda Sun Yi Barazanar Sanya Wa Majalisa Bam – Ɗan Majalisa

October 29, 2025
Sanusi Ga ‘Yan Nijeriya: Ku Dora Wa Buhari Alhakin Matsatsin Tattalin Arziki Ba Tinubu Ba

Tsoron Boko Haram Ne Ya Sa Jonathan Ya Fasa Cire Tallafin Man Fetur – Sanusi II

October 29, 2025
Firaministan Sin Ya Yi Kira Da A Kara Bude Kofa Da Karfafa Daidaita Dabarun Samar Da Ci Gaba

Firaministan Sin Ya Yi Kira Da A Kara Bude Kofa Da Karfafa Daidaita Dabarun Samar Da Ci Gaba

October 28, 2025
JIBWIS Ta Miƙa Takardar Koke Ga Gwamnatin Kaduna Kan Zargin Wasu Malamai Da Yunƙurin Tada Husuma

JIBWIS Ta Miƙa Takardar Koke Ga Gwamnatin Kaduna Kan Zargin Wasu Malamai Da Yunƙurin Tada Husuma

October 28, 2025
An Gudanar Da Taron Musamman Na Tattaunawa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa A Afrika Da Kudu

An Gudanar Da Taron Musamman Na Tattaunawa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa A Afrika Da Kudu

October 28, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.