A ranar 24 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa sun jagoranci taron tattaunawa a tsakanin shugabannin Sin da Afirka a birnin Johannesburg dake kasar Afirka ta Kudu, inda shugaba Xi ya gabatar da jawabi mai taken “yin kokari tare wajen sa kaimi ga zamanintar da kasashen Sin da Afirka da samun kyakkyawar makoma”.
Shugaba Xi ya bayyana cewa, ya kamata Sin da Afirka su yi hadin gwiwa don sa kaimi ga tabbatar da odar kasa da kasa mai adalci, da kiyaye yanayin duniya mai zaman lafiya da tsaro, da kuma raya tattalin arzikin duniya mai bude kofa wanda ke shafar kowa.
Game da tsara sabbin matakan yin hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, shugaba Xi ya bayyana cewa, Sin tana yin kira ga nuna goyon baya ga raya masana’antun Afirka, da aiwatar da shirin taimakawa Afirka wajen raya fasahohin zamani na aikin noma, da kuma shirin horar da kwararrun Sin da Afirka.
Shugaba Xi ya kara da cewa, Sin da Afirka sun yi kokari tare wajen raya sha’anin zamanintar da kasa, babu shakka za a samar da kyakkyawar makoma ga jama’arsu, da kuma zama misali yayin da ake yin kokarin raya al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya ga dukkan bil Adama. (Zainab)