A jiya Lahadi, yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping yake ziyara a kasar Faransa, ya wallafa wani bayani mai taken “Gadon akidar kulla hulda tsakanin kasashen Sin da Faransa, don tabbatar da zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki a duniya” a jaridar Le Figaro ta kasar.
A cikin bayanin, shugaba Xi ya bayyana cewa, ziyararsa a kasar Faransa a wannan karo, ta shaida manufofin Sin guda uku. Na farko, Sin tana son yada akidar kulla hulda tsakanin kasashen Sin da Faransa, don sa kaimi ga ci gaba da raya dangantakarsu. Na biyu, Sin za ta kara bude kofa mai inganci ga kasashen duniya, da zurfafa hadin gwiwa tare da sassan kasa da kasa ciki har kasar Faransa. Na uku kuwa, Sin tana son kara yin mu’amala da hadin gwiwa tare da kasar Faransa, don tabbatar da zaman lafiya da karko a duniya baki daya. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp