An kaddamar da gasar wasannin motsa jiki ta daliban jami’o’in kasa da kasa a lokacin zafi karo na 31, da daren jiya Jumma’a 28 ga watan nan a birnin Chengdu, na lardin Sichuan na kasar Sin, inda shugaba Xi Jinping ya halarci bikin kaddamar da gasar.
Rahotanni na cewa, ‘yan wasannin motsa jiki 6500, daga kasashe da yankuna 113 ne za su fafata a wasanni daban-daban. Manufofin gasar sun hada da sada zumunci, da kauna, da adalci, da tsayawa bin gaskiya, da hadin-gwiwa, da kuma nuna kwazo, manufofin da a ganin shugaba Xi, ba kawai suna samar da alkibla mai kyau ga fannin tunani ga wasannin motsa jiki na daliban jami’o’in kasa da kasa ba ne, har ma suna samar da misalai, ga shawo kan manyan sauye-sauye na duniya a wannan zamanin da muke ciki.
A wajen liyafar maraba da zuwan baki birnin na Chengdu, shugaba Xi ya gabatar da jawabi, wanda a cikin sa yake cewa, ya dace a inganta hadin-gwiwa ta hanyar gudanar da wasannin motsa jiki, don sanya kuzari ga kasa da kasa. Kaza lika ya kamata a zama tsintsiya madaurinki daya, domin shawo kan kalubalolin kasa da kasa, ciki har da sauyin yanayi, da karancin abinci, da ayyukan ta’addanci da sauransu, a wani kokari na kirkiro makoma mai haske. Al’amarin da ya bayyana ra’ayinsa na gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya, wanda kuma ya wakilci ra’ayoyi bai daya na dan Adam.
Har wa yau, shugaba Xi ya bayyana kyakkyawan fatansa ga matasan kasa da kasa, inda ya ce, yana fatan za su kalli duniya mai cike da mabambantan al’adu, bisa ra’ayoyin nuna adalci da hakuri da kauna, da kara fahimtar al’adu iri daban-daban bisa ra’ayin yin koyi da juna, a wani kokari na bayar da tasu gudummawa, wajen shimfida zaman lafiya da samar da ci gaba a duniya. (Murtala Zhang)