A yayin da Sinawa ke murnar bikin fitilu na shekarar dabbar Loong, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya amsa wasikar da daliban makarantar sakandaren Muscatine dake jihar Iowa ta kasar Amurka suka rubuta masa, inda ya aika musu da katin sabuwar shekara. A karshe watan Janairu ne dai daliban suka ziyarci kasar Sin.
A cikin wasikar, Xi ya mika gaisuwa ga malamai da daliban makarantar tare da karfafa gwiwar matasan Amurka, da su zo kasar Sin domin yin mu’amala da yin karatu.(Ibrahim)