Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana a yau Alhamis da Henry Kissinger, tsohon sakataren harkokin wajen Amurka, a gidan saukar baki na Diaoyutai na kasar Sin dake birnin Beijing.
Yayin ganawar, Xi Jinping ya bayyana cewa, shekaru 52 da suka wuce, Amurka da Sin suna kan wani muhimmin mataki kuma shugaba Mao Zedong, da firaminista Zhou Enlai da shugaba Richard Nixon da kuma Henry Kissinger, sun yi hangen nesa, sun yi zabin da ya dace na kulla hadin gwiwa tsakanin Sin da Amurka, an kaddamar da kyautata huldar Sin da Amurka, lamarin da ba kasashen biyu kadai ya amfanawa ba, har ma da sauya daukacin duniya.
Shugaban ya ci gaba da cewa, ba za su manta da daddadun abokansu ba, da ma irin gagarumar gudunmuwar da suka bayar ga raya alakar Sin da Amurka da abota tsakanin al’ummominsu.
A nasa bangare, Henry Kissinger, ya godewa kasar Sin da ta shirya ganawar a gini na 5 na gidan saukar baki na Diaoyutai, wato inda ya gana da shugabannin kasar a karon farko. Ya ce dangantakar Sin da Amurka batu ne da ya shafi zaman lafiyar duniya baki daya da ci gaban zamantakewar al’umma. (Fa’iza Mustapha)