A yau Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da takwaransa na kasar Kazakhstan Kassym-Jomart Tokayev gabanin taron kolin Sin da kasashen tsakiyar Asiya karo na biyu.
Kazalika, daga bisani duk dai a yau shugabannin biyu za su halarci bikin musayar rubutaccen daftarin hadin gwiwa tsakanin Sin da Kazakhstan.
Xi ya isa Astana, babban birnin Kazakhstan yau Litinin, domin halartar taron koli karo na biyu tsakanin kasar Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp