Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a rungumi matakan karfafa sabbin manufofin raya al’adu, da gina tsarin wayewar kai na kasa mai dacewa da zamani.
Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, kuma shugaban rundunar sojojin kasar, ya yi wannan kira ne yayin wani taro game da raya al’adun da aka gada, da wanzar da ci gaba.
Yayin taron na jiya Jumma’a, shugaba Xi ya ce matakan raya al’adu a sabon zamani, na da nufin ingiza nasarar raya al’adu, ta yadda za a gina kasa da za ta shige gaba a fannin al’adu, da karfafa wayewar kai irin na zamani na kasar Sin.
Shugaban na Sin ya kara da cewa, “Bisa karfin gwiwar da ake da shi a fannin al’adu, da amincewa da aka yi da aiki tukuru, ya zama wajibi mu dinke dukkanin kwazon mu, don samar da sabuwar al’ada mai tafiya da zamanin mu.”
Kafin halartar taron na jiya, shugaba Xi ya ziyarci cibiyar kasa ta killace tsoffin kayan dab’i da raya al’adu ko CNAPC, da kuma cibiyar nazarin tarihi ta kasar Sin. (Saminu Alhassan)