Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya sake jaddada muhimmancin fahimta da kuma yin aiki tukuru, wajen ingiza cimma nasarar zamanintarwa iri na kasar Sin.
Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban hukumar zartaswar rundunar sojojin kasar, ya yi tsokacin ne yayin bikin bude taron nazari, a cibiyar horas da JKS wadda ke karkashin kwamitin kolin jam’iyyar.
Taron ya hallara sabbin zababbun mambobi, da mambobin karba karba na kwamitin tsakiyar JKS, da kuma manyan jami’ai a matakan larduna da na ministoci. (Mai fassara: Saminu Alhassan)