Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jadadda muhimmancin aiwatar da sauye sauye, da kafa sabbin ginshikai, da ingiza himma da kwazo, wajen zamanantar da harkar shari’a, da harkokin gabatar da kararraki, da fannin tsaron al’umma.
A baya bayan nan ne dai shugaba Xi, ya bayar da muhimmin umarni, game da ayyukan da suka shafi shari’a, da harkokin gabatar da kararraki, da fannin tsaron al’umma. A madadin kwamitin kolin JKS, shugaba Xi ya mika sakon gaisuwa, da godiya ga daukacin ‘yan sanda, gabanin ranar ‘yan sandan janhuriyar jama’ar kasar Sin, wadda za a yi bikin ta a jibi Talata 10 ga watan nan na Janairu. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp