A yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika sakon jejeto ga Mohamed Menfi, shugaban majalisar gudanarwar Libya, dangane da mahaukaciyar guguwar da ta afkawa kasar Libya.
A cikin sakon nasa, shugaba Xi ya ce, ya kadu matuka da samun labarin mahaukaciyar guguwar da ta afkawa kasar, lamarin da ya janyo hasarar rayuka da dukiyoyi.
A madadin gwamnati da al’ummar Sinawa, Xi ya yi jimami matuka ga wadanda abin ya shafa, tare da nuna jaje ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da ma wadanda suka jikkata. Haka kuma shugaba Xi ya bayyana imaninsa cewa, ko shakka babu al’ummar Libya za su shawo kan illar iftila’in.
Ma’aikatar lafiya ta Libiya ta bayyana yau cewa, akalla mutane 2,300 ne suka mutu yayin da sama da dubu biyar suka bace a birnin Derna na kasar, bayan da wata mummunar ambaliyar ruwa da ta mamaye gabashin kasar a ranar Lahadin da ta gabata.(Ibrahim)