Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jinjinawa aiki tukuru da babban jami’in gudanarwar yankin musamman na Hong Kong John Lee ya yi. Shugaban na Sin yana mai bayyana sabuwar gwamnatin yankin musamman na HK, a matsayin wadda ta taka rawar gani a fannin inganta tsaron kasa, da farfado da tattalin arzikin yankin.
Ya bayyana hakan ne a yayin ganawa da mista John Lee a jiya Jumma’a a birnin Beijing. Ya ce a yanzu haka, Hong Kong na samun ci gaba bisa daidaito kan turba mai nagarta, bisa salon “Kasa daya tsarin mulkin biyu”. Daga nan sai ya jinjinawa Mr. Lee bisa kokarin sa na dora HK kan sabon yanayi, wanda ya baiwa masu kishin kasa damar jagorantar yankin.
A lokacin ganawar tasu, shugaba Xi ya saurari rahoto daga John Lee, dangane da yanayin da yankin Hong Kong ke ciki, da kuma ayyukan hukumar yankin.
Har ila yau a dai jiyan, shugaba Xi ya gana da babban jami’in gudanarwar yankin musamman na Macao Ho Iat Seng, wanda shi ma ke ziyarar aiki a birnin Beijing. Inda shugaban na Sin ya saurari yanayin da yankin Macao ke ciki, da kuma ayyukan hukumar yankin.
Shugaba Xi ya ce, cikin shekarar da ta gabata, Ho ya jagoranci yankin na musamman, inda ya gudanar da ayyuka cikin himma da gwazo, matakin da ya wanzar da daidaito a dukkanin sassan rayuwar al’ummar yankin.
Shugaba Xi ya ce gwamnatin tsakiya ta kasar Sin, tana da cikakkiyar masaniya game da kwazon Mr. Ho, da ma himmar gwamnatin sa ta kai yankin Macao ga nasara. (Saminu Alhssan)