Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a kara azama wajen ingiza muhimmiyar rawa da kundin tsarin mulki ke takawa a fannin jagorancin kasa.
Cikin wani umarnin shugaba da ya gabatar a Litinin din nan, albarkacin ranar kundin tsarin mulkin kasa karo na 10 da ake bikin ta a yau din, shugaba Xi ya jaddada muhimmancin martaba iko, da kimanta darajar kundin tsarin mulkin kasa, yayin da ake yayata manufofin ingantawa da bunkasa shi.
- Shugaba Xi Ya Jaddada Muhimmancin Gaggauta Gina Shanghai Zuwa Birnin Zamani Na Gurguzu
- Gwamnatin Tarayya Ta Nemi Kamfanin Nokia Ya Zuba Jari Wajen Karfafa Kimiyyar Sadarwa A Nijeriya
Ya ce kundin tsarin mulkin kasa shi ne tushen ayyukan shari’a, wanda jam’iyya ke amfani da shi wajen jagorancin kasa, kana shi ne tsarin shari’a na koli ga siyasa da zaman rayuwar al’ummar kasa.
Daga nan sai shugaban na Sin ya jaddada muhimmancin kara azama wajen kyautata tsarin shari’a na gurguzu mai halayyar musamman na Sin, wanda ke da kundin tsarin mulkin kasa a matsayin jigonsa, tare da ci gaba da kyautata yadda ake aiwatarwa da sanya ido kan sa. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp