Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a samar da sabbin nasarori wajen kare muhallin halittu tare da ci gaba mai inganci a Rawayen Kogi.
Xi Jinping wanda kuma shi ne sakatare janar na kwamitin kolin JKS, kuma shugaban hukumar koli mai kula da aikin soji ta kasar, ya bayyana haka ne a yau, yayin wani taro da ya kira a Lanzhou, babban birnin lardin Gansu na arewa maso yammacin kasar Sin.
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Matafiya A Babbar Hanyar Gusau-Funtua
- Kotu Ta Bada Belin Masu Zanga-Zangar Tsadar Rayuwa Kan Naira Milyan 10 Kowanensu
Da yammacin jiya Laraba ne shugaba Xi Jinping ya kammala rangadi cikin nasara a sassan unguwar Zaolin ta yamma dake gundumar Anning, da yankin gadar Zhongshan, duk a cikin birnin Lanzhou na lardin Gansu, dake yammacin kasar Sin.
Yayin rangadin, shugaba Xi ya nazarci ayyukan samar da saukin rayuwa, da na hidimomi da aka samarwa al’ummun wuraren, tare da na karfafa jagorancin kula da jin dadin jama’a, da ingiza kare muhallin halittu a yankunan rawayar kogi. (Fa’iza Mustapha, Saminu Alhasan)