A yau Alhamis ne shugaban kasar Sin, kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya ziyarci birnin Cangzhou na lardin Hebei dake arewacin kasar.
Yayin ziyarar ta sa, Xi ya ziyarci gonakin alkama, inda ya ganewa idanun sa yadda ake noman iri masu jurewa fari, da yanayin kasa mai yanayi na daban. Kaza lika ya ziyarci tashar hakar kwal, domin ganin yadda ake gudanar da ayyuka, da tsara matakan ci gaban fannin. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp