Kakakin ma’aikatar cinikayyar kasar Sin ya ce a gobe Juma’a, shugaban kasar Xi Jinping zai gabatar da jawabi ta kafar bidiyo, yayin bude bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin ko CIIE karo na 5 a birnin Shanghai, da kuma dandalin kasa da kasa na tattauna batutuwan da suka shafi tattalin arziki na Hongqiao.
Mashirya baje kolin sun ce wakilai daga kasashe 145, da yankuna da hukumomin kasa da kasa za su shiga a dama da su, a baje kolin da zai gudana tsakanin ranekun 5 zuwa 10 ga watan nan na Nuwamba. Cikin manyan kamfanoni 284 da za su baje hajojinsu a bana, akwai wadanda ke cikin jerin kamfanoni mafiya girma 500 na duniya.
A bana, ana sa ran bude sabon sashen baje kolin hajoji, daga kamfanonin samar da irin shuka, da na fasahohin kwaikwayon tunanin bil Adama, baya ga daruruwan sabbin masu sayayyar albarkatun gona, da hajojin fasaha, da sauran ayyukan hidima.
Bikin baje kolin CIIE, shi ne irinsa na farko a duniya, wanda wata kasa ke gudanarwa da nufin hallara masu shigo da hajoji daga waje, wanda kuma ke gudana a birnin Shanghai na gabashin kasar Sin duk shekara, tun daga shekarar 2018. (Saminu Alhassan)