Bayan kwanaki da aka kwashe ana cece-kuce kan yadda shugaban kasa Bola Tinubu ya yi afwa ga wasu nau’ikan fursunoni, ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a, ya fayyace cewa, babu wani cikin fursunonin da aka amince da yi masa afuwa, yana mai cewa, komai zai iya canjawa.
Ofishin ya ce, tsarin har yanzu yana kan matakan gudanarwa na karshe, don tabbatar da cewa, an bi ƙa’idojin da suka dace kafin a tabbatar da afuwar.
Ya yi nuni da cewa, tsarin tantancewa, abu ne mai muhimmanci a tsarin yin afuwa kuma ya tabbatar da kudirin gwamnati na tabbatar da yin gaskiya da bin diddigin komai.