A kwanan baya ne shugaban kasar Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ya zanta da wakiliyar CMG yayin ziyararsa a kasar Sin, inda ya yi tsokaci cewa, kasar Sin ta samarwa Aljeriya tallafi a lokacin da take fama da matsala mai tsanani, kuma zumuncin dake tsakanin kasashen biyu ba zai taba sauyawa ba ko kadan, Ya kuma yaba da babbar rawar da kasar Sin ta taka wajen kyautata huldar dake tsakanin kasashen Larabawa da kasar Iran.
Ya kuma yi imanin cewa, sada zumunta tsakanin al’ummomin kasashe daban daban shi ne abu mafi kyau a duniya.
Haka zalika, shugaban Aljeriya ya kara da cewa, yana adawa da duk wani nau’in na nuna fin karfi, yana mai cewa, ya dace daukacin kasashen duniya su samu ci gaba bisa ‘yancin kanta.
Ban da haka yana fatan kasarsa za ta shiga tsarin hadin gwiwa na kasashen kungiyar BRICS, ta yadda za ta ba da gudummowarta wajen gina duniya mai adalci da kyakkyawar makoma ta bai daya. (Mai fassara: Jamila)