A yayin da al’ummar jihar Sakkwato suka fito zaben shugabannin ƙananan hukumomi 23 a ranar Asabar, shugaban jam’iyyar APC na jiha, Honarabul Isa Sadik Achida ya bayyana gamsuwa da yadda zaben ke gudana.
A tattaunawa da manema labarai bayan jefa kuri’a a garin Achida, ya bayyana gamsuwa da tsarin da hukumar zabe ta jiha ta aiwatar a zaben. Haka ma ya bayyana jin dadin yadda jama’a suka fito sosai a karamar hukumar domin sauke ‘yancin su na zaben wadanda suke ra’ayi.
- Ƙaramin Ministan Tsaro Da Manyan Shugabannin Soji Sun Isa Sokoto Domin Fatattakar ‘Yan Bindiga
- Kotu Ta Sanya Rana Kan Batun Tsige Ganduje A Matsayin Shugaban APC
Ya bayyana tabbacin samun nasarar jam’iyyarsa ga dukkanin kujeru 23 da kansiloli bisa abin da ya kira dimbin nasarorin da suka samu a gwamnatance a mulkin sama da shekara daya.
Shi ma da yake nashi bayanin, kwamishinan yaɗa labarai, Sambo Bello Danchadi ya ya bawa al’ummar jihar kan yadda suka fito gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali ba tare da wata hayaniya ba. Ya shawarci jami’an tsaro da su kasance cikin shiri domin tabbatar da zaben ya gudana yadda aka tsara ba tare da wata matsala ba
Dan takarar shugaban karamar hukumar Wurno, Abba Isa Achida ya yaba da yadda masu zabe suka fito da yawa a karamar hukumar. Haka ma ya bayyana tabbacin samun nasarar lashe zaben tare da cewar idan ya samu nasara zai aiwatar da ayyukan ci-gaban al’umma.
Jam’iyyar PDP a jihar ta ƙauracewa shiga zaben bisa zargin rashin samun adalci daga hukumar zaben ta jiha wanda hakan ya sa zaben ke gudana ba tare da wani tarnaki ga jam’iyyar APC ba.