A ranar 1 ga watan Janairun 2024, shugaban babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG Shen Haixiong, ya gabatar da jawabin murnar sabuwar shekara ga masu bibiyar CMG ta kafar talabijin ta CGTN, da gidan radiyon kasar Sin CRI da kuma kafar yanar gizo.
‘Yan uwa da abokai,
A yayin da hasken farko na ranar sabuwar shekara ya bayyana, mun sanya kafa cikin shekarar 2024 cike da fatan nasara. Ina gabatar muku gaisuwa ta daga nan birnin Beijing!
- Shugabannin Sin Da Rasha Sun Tura Wa Juna Sakwanni Don Murnar Sabuwar Shekara
- Sin Ta Mai Da Hankali Ga Kimiyya Da Fasaha
A shekarar 2023, shawarar “Ziri daya da hanya daya” ko BRI, ta cika shekaru 10 cikin karsashi, kasar Sin da duniya baki daya na samun ci gaba tare. A wannan hanya ta neman wadata, CMG ta ci gaba da yayata musaya tsakanin mabambantan wayewar kai, tare da cimma nasarori masu tarin yawa, ta hanyar shiga a dama da ita a harkokin duniya daban-daban.
A bana, mun sake daga matsayin kirkire-kirkire karkashin manufar “Tunani + Nuna Basira + Fasahohi” zuwa wani sabon mataki. Mun watsa shiri mai lakabin “Kalaman Magabata Na Xi Jinping (Zango na 2)” cikin harsuna da dama a kasashe sama da 80. Mun watsa shirye shiryen raya al’adu da dama masu wakiltar wayewar kan kasar Sin da sauran sassan duniya. Yawan wadanda suka kalli shirye-shiryen gasar wasannin motsa jiki na kasashen Asiya ta Hangzhou ta shafuka daban daban na yanar gizo, ya kai biliyan 41.4 wanda hakan ya kai matsayin koli a tarihi.
A bana, hadin gwiwar mu ta haifar da kyakkyawan sakamako. Tsoffin abokan mu sun zo haka ma sabbin abokan hulda. Mun sanya hannu kan yarjeniyoyin hadin gwiwa har 58 tare da kafofin shirye-shirye na kasa da kasa, kana mun gudanar da karo na biyu na taron kirkire-kirkire a fannin ayyukan kafofin watsa labarai, da taron hadin gwiwar kafofin watsa labarai na kungiyar kasashen ASEAN, da taron hadin gwiwar kafofin watsa labarai na kasashen Afirka.
Karkashin ayyuka 51 na “Zamanantar da Sin da duniya “, da kuma bikin baje koli 8 na “Tafiya a tafarkin wayewar kai” wanda aka yi a sassan kasa da kasa, mun yi aiki tare da abokai na sassan duniya daban daban, inda muka bayyana kyakkyawar surar zamanantar da duniya bisa tafarkin ci gaba cikin lumana, da hadin gwiwar cimma moriya tare, da samar da wadatar bai daya.
Duniya a yau na fama da tashe-tashen hankula. Akwai matukar bukatar zaman lafiya, da ci gaba, da hadin gwiwa da cimma sakamako. Muna farin cikin ganin karin abokai na kasa da kasa na nuna fahimta, da lura tare da goyon bayan ra’ayoyi da mahangar kasar Sin.
A gefen taron APEC, mun gudanar da taron tattaunawa da mu’amalar al’adu a tsakanin Sin da Amurka a birnin San Francisco na Amurka, wanda ya samu kyakkyawar maraba. Mr. Harry Moyer, dattijon da ya kai shekaru 100, kuma mamba a kungiyar kawance ta “Flying Tigers”, ya kasance cikin wadanda suka halarci taron. Ya kuma shaida min cewa mahangar shugaba Xi game da gina al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil Adama, ta karbu a zukatan dukkanin al’umma. Bayan dawowa gida, na samu sakon kati, da kwallon taswirar duniya, da wasu kayan kawa da wasu yaran makarantar midil ta Lincoln dake Amurka suka aiko min. Kalli irin wannan kyauta, na yi farin ciki da tunanin yaran na zaman lafiya, da kauna, da kayatarwa da musaya tare da mu.
A matsayin ta na babbar kafar watsa labarai ta duniya ta fuskar girma da fadin sassa, CMG ta cika shekaru 5 da kafuwa, tana kuma kara karfi sannu a hankali. A bara, mun kammala bude reshensa na 191 a ketare, tare da kafa tsarin watsa shirye shirye dake hade kasashe da yankunan duniya 67. Kaza lika a karon farko, adadin masu kallo kafar CGTN a kasashen duniya sun haura miliyan 700. Kafar CGTN ta sha zama ta farko a duniya a fannin samar da labarai masu dumi-dumi game da manyan batutuwan kasa da kasa. Game da tafarkin gina sabon salon kafar watsa labarai mai karfi a duniya, za mu ci gaba da gaggauta aiwatar da burin mu na “gabatar da shirye-shirye masu inganci”.
Abokai, shekarar 2024 shekara ce ta dabbar “Loong” bisa kalandar gargajiyar kasar Sin.
Dabbar “Loong” ta kunshi tatsuniya game da wayewar kan kasar Sin, wanda ke wakiltar ruhin koyi daga kowa da kowa, da haifar da gajiya ga komai, da cimma matsaya guda yayin da ake kiyaye banbance banbance, da zama tare cikin jituwa.
Al’ummar Sinawa, ta ci gaba kan sabon tafarki, yayin da take bikin cika shekaru 75 da kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin a wannan shekara ta “Loong”. CMG zai ci gaba da gabatar da labarai game da kasar Sin da ma duniya ga dukkanin bil Adama, zai ci gaba da rubuta sabbin babuka game da wayewar kan bil Adama, tare da yin maraba da sabuwar bazara!
Ina yiwa daukkanin al’ummar duniya fatan alheri a wannan sabuwar shekara! (Saminu Alhassan)