Shugaban kasar Costa Rica Rodrigo Chaves, ya bayyana gamsuwar sa, game da shawarar “Bunkasa ci gaban duniya” da ta “wanzar da tsaron duniya”, wadanda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar.
Shugaba Chaves, wanda ya bayyana hakan yayin wata zantawar baya bayan nan da ya yi da kafar CMG, ya ce, “A ganina babu wanda zai soki wannan shawarwari. Fatan mu shi ne rayuwa a duniya mai tsaro, wadda babu tashe-tashen hankula a cikin ta, kuma cikin yanayi na zaman lafiya, yayin da al’ummun duniya ke kokarin cimma nasarorin wanzar da zaman lafiya da lumana da samun farin ciki”.
Kaza lika, shugaban na Costa Rica, ya ce ya amince da manufofin dake kunshe cikin shawarwarin da shugaba Xi ya gabatar. Yana mai fatan za a kai ga cimma tsaro da zaman lafiya a duniya ta hanyoyin lumana.
Ya ce bisa tarihin samar da ci gaban kasa da kasa, idan aka samu babban gibi a tsakanin al’umma, hakan na haifar da rashin daidaito, haka kuma abun yake a duniya baki daya.
Don haka, kalaman shugaba Xi suka kasance masu matukar ma’ana, wato cewa ta hanyar samun wadata da ci gaba, da tsaro ne kadai za mu samu ingantacciyar rayuwa, kuma mu bar wa ‘yan baya kyakkyawar duniya. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp