Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya bayyana manufar kasar Sin ta soke biyan harajin kwastam ga kasashen Afirka, a matsayin wata dama ta musamman da nahiyar za ta yi amfani da ita wajen samun ci gaba mai yawa.
Da yake amsa tambayoyi da yammacin ranar Laraba daga kafofin yada labarai, a yayin babbar ganawarsa ta farko da ‘yan jarida tun bayan da ya dare karagar mulki a watan Janairu, Mahama ya bayyana cewa, rangwamen da aka samu daga kasar Sin, wani albishir ne ga Afirka na kara yawan kayayyakin da take fitarwa zuwa kasar da ke yankin Asiya.
Mahama ya ce kasashen Afirka, ciki har da Ghana, su ma za su iya habaka sarrafa kayayyakinsu don fitarwa zuwa kasuwannin kasar Sin mai yawan jama’a biliyan 1.4.
Mahama ya kuma zargi Amurka da kawo cikas ga harkokin kasuwanci da aka kafa tsarinsu bisa dokokin da dukkan kasashen duniya suka yi aiki tukuru wajen samar da su ta hanyar shawarwari daban-daban. Yana mai nuni da cewa, “Babu mai yin nasara a yakin haraji. Abin takaici ne yadda Amurka ke wargaza tsarin kasuwancin duniya baki daya.”
A baya-bayan nan dai, kasar Sin ta ba da sanarwar fadada manufarta ta soke biyan harajin kwastam domin ta karade dukkan kasashen Afirka 53 da suka kulla huldar jakadanci da ita. (Abdulrazaq Yahuza Jere)