Shugaban IOC Thomas Bach, ya ba da jawabi ta kafar bidiyo ga mahalarta dandalin wayewar kan Bil Adam na kasa da kasa na Nishan karo na 10 a jiya Laraba inda ya ce burin dandalin ya yi daidai da na Olympic, wato kara fahimtar mabambantan al’adun kasa da kasa ta hanyar shawarwari bisa tushen mutunta juna.
Wannan ne dai karon farko da aka kebe reshen al’adun wasannin motsa jiki a dandalin, mai taken “Al’adun gargajiya na kasar Sin da ruhin Olympic”, wanda hakan ya samu yabo daga mista Bach.
A cewarsa, lokacin da Le baron Pierre De Coubertin, wanda ya kafa gasar Olympic ya farfado da ita, ya mai da gasar wani dandalin kara tuntubar al’umommmin kasa da kasa. Kuma burin Nishan ya yi daidai da hakan. Kaza lika, mista Bach ya yi fatan za a kara fahimtar mabambantan ala’dun al’umommin kasa da kasa ta hanyar kara tuntubar juna, bisa tushen yayata wayewar kan Confucius, shahararren malami a tarihin Sin dake da tunani mai zurfi. (Amina Xu)