Shugaban karamar hukumar Lokoja, Hon. Muhammed Danasabe Muhammad ya rasu.
Hon. Danasabe ya rasu a safiyar Juma’a a asibitin Shifa da ke Lokoja, bayan wata gajeruwar rashin lafiya da yi.
- Zaɓen Bayelsa, Imo da Kogi: Shugaban INEC Ya Ja Kunnen Ma’aikata Su Yi Aiki Da Gaskiya
- Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Natasha A Matsayin Sanatan Kogi Ta Tsakiya
Za a yi jana’izar Danasaben a makabartar Musulmi ta Unguwar Kura bayan sallar Juma’a.
Marigayi shugaban karamar hukumar, jarumi ne kuma gwarzo a fagen siyasar jihar, ya taka muhimmiyar rawa a zabukan da suka gabata, rasuwarsa za ta zama babban rashin da zai wuyi a iya cike gurbinsa musanman a jam’iyyar APC.
Ya rasu ya bar mahaifiyarsa da mace daya da ’ya’ya.