Shugaban karamar hukumar Akwanga a jihar Nasarawa, Safiyanu Isah Andaha wanda wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da shi, ya kubuta daga hannun yan bindigar.
An bayyana cewa, Andaha ya shaki iskar ‘yanci ne a daren ranar Talata bayan ‘yan uwansa sun biya kudin fansa naira miliyan 10 ga wadanda suka yi garkuwa da shi.
- Mutane Sama Da 90% Sun Nuna Damuwa Kan Yadda Kasafin Kudin Tsaron Amurka Da Japan Suka Kai Sabon Matsayi
- Gwamnan Kano Ya Karyata Jita-jitar Rikicinsa Da Sakataren Gwamnatin Jihar
An sake shi ne tare da wani shahararren dan kasuwa kuma abokinsa, Alhaji Adamu Tanko.
A baya LEADERSHIP ta rahoto cewa, tun farko masu garkuwa da shugaban karamar hukumar sun bukaci naira miliyan 50 a matsayin kudin fansa domin su sake shi.
A cewar majiyar, bayan tattaunawa mai zurfi ta hanyoyin wayar salula, wadanda suka yi garkuwar sun bayyana cewa, ba za su sake shugaban ba akan kudi kasa da Naira miliyan 10 ba.