Kwanan baya, shugaban kasar Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema Mbasogo, ya zanta da wakilin CMG a shirinsa na “Leaders Talk”, inda ya bayyana cewa, ya zama dole shugabannin kasashen Afirka su yi tunani a kan ta yaya za a kyautata kasashensu, don in ba haka ba, kasashen ba za su ci gaba ba, kuma wannan dalili ne da ya sa kasar Equatorial Guinea ta amince, tare da aiwatar da shawarar “ziri daya da hanya daya” tare da kasar Sin, kasancewar kasar Sin ta farko da take taimakawa Equatorial Guinea, da ma nahiyar Afirka baki daya. Don haka, shawarar “ziri daya da hanya daya”, ita ce mafita ga kasashen Afirka wajen samun ci gabansu, da fitar da kansu daga yanayin da suke ciki na rashin ci gaba da wahala.
Da yake magana a kan zargin wai “Sin na kafa sabon mulkin mallaka da tarkon bashi a Afirka”, da wasu kasashen yammacin duniya suke yayatawa, shugaban ya ce, shafa wa kasar Sin bakin fenti kawai suke yi, kuma ya kamata wadannan kasashen yamma su ji kunya, don yanzu gudummawa kalilan ne Afirka ke samu daga wajensu.
Ya kara da cewa, don neman samun gudummawar, ba mu da zabi illa mu amince da sharudan siyasa da suka gindaya mana, wadanda a gaskiya suna lalata kwanciyar hankalin kasashenmu.
Ya ce, kasashen yamma ne suka yi wa kasashen Afirka mulkin mallaka, a maimakon kasar Sin. Don haka, sukan da suke yi wa kasar Sin, a hakika don neman dalike kasar ne, ta yadda kasar za ta kasa ci gaba da taimaka wa Afirka wajen tabbatar da ci gabanta. Amma mun gano gaskiyar lamarin, wato kasar Sin ita ce babbar aminiyarmu. (Lubabatu)