A ‘yan shekarun nan, kasar Sin na kokarin samar da dabaru, gami da hikimominta ga dukkanin duniya, ciki har da shawarar “ziri daya da hanya daya”, da kuma ra’ayin gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya, gami da shawarar samar da ci gaban duniya, wadda shugaban kasar Xi Jinping ya bullo da ita. Shin ko wace irin gudummawa wadannan hikimomi na kasar Sin ke bayarwa, a fannin daidaita matsalolin dake addabar dukkanin duniya?
Kwanan nan, shugaban kasar Guyana, Mohamed Irfaan Ali, ya zanta da babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin ko kuma CMG a takaice, inda ya bayyana cewa, duniya na fuskantar matsalolin da suka shafi yanayi, da makamashi da abinci, baya ga matsalar rashin daidaito.
Kamar yankin Caribbean, duk da cewa kasashen dake wannan yanki ba sa fitar da hayaki mai gurbata yanayi sosai, amma sun fi jin radadin gurbatar yanayi a jikinsu. Haka ma a fannin abinci. Sai kuma a bangaren makamashi, kasashe masu tasowa da dama ba su samu tabbacin tsaron makamashi ba, kuma mutane da yawa ba sa samun makamashin wutar lantarki. Kuma in dai babu makamashi, to fa babu fasahohi, kuma in babu fasahohi, babu yiwuwar samun sauye-sauye. Kana rashin sauye-sauye, zai dakile samun makoma mai haske.
Don haka, a ganin shugaba Mohamed Irfaan Ali, a wadannan fannoni hudu, wato yanayi, da mkamashi, da abinci, da kuma daidaito, kasar Sin za ta iya samar da jagorancin ra’ayi, za ta kuma taka muhimmiyar rawa a duniya. A cewarsa, idan aka samu hikimomi, gami da goyon-baya daga kasar Sin, za’a taimakawa duniya, musamman kasashe masu tasowa, wajen shawo kan wadannan matsaloli. (Murtala Zhang)