A kwanan nan ne aka rufe taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai ko SCO a takaice, a birnin Tianjin dake arewacin kasar Sin, inda shugaban kasar, Xi Jinping ya gabatar da shawarar tsarin inganta jagorancin duniya. Wakiliyar babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, ta zanta da shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian, wanda ya halarci taron, inda ya ce, ana amfani da ma’aunai biyu a halin yanzu a duk duniya. A cikin shawarar tsarin inganta jagorancin duniya da shugaba Xi Jinping ya gabatar, akwai wani muhimmin bangare na gudanar da harkokin duniya bisa dokokin kasa da kasa, wato ya kamata a mutunta ka’idoji.
Masoud Pezeshkian, ya ce bai kamata a aiwatar da ma’aunai biyu a fannin dokokin kasa da kasa ba, wato duk wata kasa, mai fama da talauci ko mai hannu da shuni, mai tasowa ko mai karfin tattalin arziki, babba ko karama, ya kamata a mutunta ta cikin adalci. Amma har yanzu ba a kai ga cimma wannan buri ba.
A ganinsa, ya dace sassan kasa da kasa su girmama wannan ka’ida, ta yadda za a iya aiwatar da shawarar tsarin inganta jagorancin duniya. Ya ce a hakikanin gaskiya, idan ana son yin watsi da ra’ayin nuna bangaranci, ya kamata a bi tsarin da aka kafa, gami da yarjeniyoyin da aka daddale a wajen taron kolin kungiyar SCO na wannan karo, tare da aiwatar da su a zahirance. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp