Shugaban kasar Sin Xi Jinping, gami da takwaransa na kasar Kazakhstan, Kassym-Jomart Tokayev, sun gabatar da sakwanni don murnar kaddamar da “shekarar yawon bude ido ta Kazakhstan” ta bana a kasar Sin.
An kaddamar da “shekarar yawon bude ido ta Kazakhstan” ta 2024 ne jiya Jumma’a a birnin Beijing, bikin da ma’aikatar al’adu da yawon shakatawa ta kasar Sin, da ma’aikatar yawon shakatawa da wasannin motsa jiki ta kasar Kazakhstan suka gudanar cikin hadin-gwiwa. (Murtala Zhang)