Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon taya murnar cikar kungiyar INBAR shekaru 25 da kafuwa, da kuma taron kasa da kasa na biyu kan itatuwan gora da Rattan.
Cikin sakon da ya aike a Litinin din nan, shugaba Xi ya ce tun kafuwar kungiyar kasa da kasa ta lura da batutuwan da suka shafi itatuwan gora da Rattan ko INBAR, kungiyar na kara himma wajen bada kariya, da bunkasawa, da kiyaye amfani da albarkatun itatuwan biyu, ta kuma taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa kare muhallin halittu a matakin kasa da kasa, da wanzar da ci gaba.
Shugaba Xi ya kara da cewa, gwamnatinsa da kungiyar INBAR, sun yi hadin gwiwar aiwatar da shawarar bunkasa ci gaban duniya, sun kuma kaddamar da manufar nan ta “Amfani da itacen gora maimakon roba” da nufin yayata rage gurbata muhalli ta amfani da robobi, da shawo kan mummunan tasirin sauyin yanayi, da gaggauta aiwatar da ajandar MDD ta wanzar da ci gaba nan da shekarar 2030. (Saminu Alhassan)