Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika da wasikar taya murna, ga bikin cika shekaru 50 da fara hadin gwiwa a tsakanin Sin da kungiyar kare hakkin mallakar fasahohi ta duniya ko WIPO.
Cikin wasikar da ya aike a yau Laraba, Xi Jinping ya nuna cewa, cikin shekaru 50 da suka wuce, kasar Sin ta tsaya tsayin daka kan kiyaye tsarin mallakar fasahohi na duniya da ke tsakanin bangarori da dama, kuma ta yi ta fadada hadin gwiwa da kungiyar kare hakkin mallakar fasahohi ta duniya (WIPO), tare da cimma gagaruman nasarori.
Kaza lika kasar Sin na dora matukar muhimmanci ga aikin kare hakkin mallakar fasahohi, inda ta inganta dokokin kare hakkin mallakar fasahohi, da ma tsarin kula da hakkokin, baya ga kuma yadda take dada kyautata yanayin kirkire-kirkire da na kasuwanci.
Shugaban na Sin ya kara da cewa, kasarsa na son inganta hadin gwiwarta da kungiyar ta WIPO, don kara tabbatar da adalci a tsarin kare hakkin mallakar fasahohi na duniya, da ma samar da alherai ga ’yan Adam. (Lubabatu Lei)