A jiya Laraba da safe, an samu ruftawar wani bangare na babbar hanyar mota dake birnin Meizhou na lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin. Ya zuwa safiyar ranar 2 ga wata, lamarin ya riga ya haddasa rasa rayukan mutane 36, kana wasu mutane 30 kuma suna jinya a asibiti.
Bayan abkuwar lamarin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da umarni ga hukumomi masu kula da aikin ceto, inda ya ce ya kamata a yi iyakacin kokarin ceton rayukan mutane, da kula da wadanda suka jikkata, gami da daidaita al’amura dake biyo baya yadda ake bukata. Kana ya bukaci a gyara titin mota da ya lalace, don maido da zirga-zirgar motoci a wurin cikin sauri.
A cewar shugaban, yanzu lokaci ne da Sinawa suke hutun bikin ranar ‘yan kwadago, da yawan yin zirga-zirga. Kana a wasu yankunan kasar Sin za a samu babban ruwan sama, wanda ka iya haddasa abkuwar hadari da bala’i. Saboda haka, kamata ya yi, hukumomi masu ruwa da tsaki su yi kokarin sauke nauyin dake bisa wuyansu, da sanya ido kan yanayin da mabambantan ayyuka suke ciki, da kyautata tsarin da ake amfani da shi wajen tinkarar wasu al’amuran da suka abku ba zato ba tsammani, da kula da wurare da fannoni da ka iya samun matsala, don tabbatar da tsaron jama’a, da zaman karko na al’umma. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp