Shugaban kasar Sin ya yabawa gagarumar gudunmuwar da marigayi Deng Xiaoping ya bayar tare da kira da a daukaka tunanin gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin da Deng ya kirkiro, yayin da marigayin ke cika shekaru 120 da zuwa duniya, a yau Alhamis.
Da yake jawabi ga wani taron domin ranar, Xi Jinping, wanda shi ne sakatare janar na kwamitin koli na JKS kuma shugaban hukumar koli ta sojin kasar, ya ce wajibi ne kasar ta ci gaba da nazari da aiwatar da tunanin Deng Xiaoping.
A cewar shugaba Xi, Deng ya bada gagarumar gudunmuwa ga JKS da kasar Sin da al’ummarta da ma duniya baki daya. Yana mai cewa, nasarorin da Deng ya samu ba za a taba mantawa da su a tarihi ba, kuma za su ci gaba da karfafa gwiwar zuri’o’i masu zuwa. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp