Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da mai masaukin bakinsa shugaba Vladimir Putin na Rasha a Litinin din nan a birnin Moscow.
Shugaba Xi na ziyarar aiki ne a Rasha tsakanin ranaikun 20 zuwa 22 ga watan nan, bisa gayyatar da shugaba Putin ya yi masa.
Cikin rubutaccen jabawin da ya gabatar bayan ya isa filin jirgin saman a Moscow, shugaba Xi ya ce, yau nake cika shekaru 10, bayan ziyarar aiki ta farko da na kawo Rasha a matsayin shugaban kasar Sin, inda tare da shugaba Putin na Rasha, muka bude sabon babin dangantakar kasashen biyu. Cikin shekaru sama da 10 da suka gabata, Sin da Rasha sun ci gaba da yaukakawa, da bunkasa alakar su bisa tushen rashin kulla kawance don mayar da wata kasa saniyar ware, da kaucewa fito na fito da kin far wa wani bangare na uku, sun kuma gina sabon salon alakar manyan kasashe bisa martaba juna, da zaman jituwa, da cimma moriyar hadin gwiwa. Ribar kyakkyawar dangantakar Sin da Rasha, ta haifar da moriya mai yawa ga al’ummun sashen biyu, tare da samar da gudummawa ga ci gaba, da bunkasar duniya baki daya.
Jawabin ya kuma fayyace cewa, Sin da Rasha dukkanin su manyan kasashen duniya ne, kuma mambobin dindindin a kwamitin tsaron MDD, wadanda ke taka muhimmiyar rawa a harkokin kasa da kasa. Yayin da ake fuskantar halin rashin tabbas da sauye sauye a duniya, Sin a shirye take ta ci gaba da aiki tare da Rasha, wajen kiyaye ka’idojin alakar kasa da kasa, da nacewa ci gaban dangantakar dukkanin sassa, da bunkasa akidar samar da ci gaba ta mahangar sassa daban daban, da gudanar da huldar kasa da kasa bisa dimokaradiyya, da yayata kyakkyawan jagorancin duniya bisa turbar adalci da dacewa.
Bugu da kari, a yau Litinin 20 ga wata, a gabannin fara ziyararsa ta aiki a tarayyar Rasha, aka wallafa bayanin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya rubuta, mai taken “Tinkarar kalubaloli tare: bude wani sabon babi na kara hadin kan Sin da Rasha, da samun bunkasuwa tare” a “Jaridar Rasha”, da shafin yanar gizo na kamfanin dillancin labarun kasar.
Bayanin ya nuna cewa, bunkasuwar dangantakar kasashen biyu, na bisa karfi daga zuciyoyin su a cikin daddaden lokuta. A cikin shekaru 10 da suka gabata, hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a fannoni daban daban ta samu bunkasuwa sosai.
A bara, rikicin dake tsakanin Rasha da Ukraine ya tsananta. Sin na nacewa matsayin nuna adalci, da ingiza yin shawarwari tsakanin bangarorin masu ruwa da tsaki. Sin ta gabatar da takardar matsayin Sin game da warware rikicin Ukraine ba da dadewa ba, inda ta shigo da abubuwa masu dacewa da mahangar bangarori daban-daban. Sin ta yi imanin cewa, ba shakka za a iya warware rikicin, da tabbatar da kwanciyar hankali da tsaron duniya bisa hanyar da ta dace, idan bangarori masu ruwa da tsaki su hada kansu, da nacewa ga nuna adalci da daidaito, da daukar matakai masu dacewa.
Shugaba Xi ya kara da cewa, idan ana son taka rawa wajen warware batutuwan dake wakana a duniya, dole ne da farko, a daidaita matsalolin dake kasancewa a cikin gida yadda ya kamata. Ya ce “Muna cike da imanin cewa, Sin za ta ci gaba da ingiza sha’anin zamanintarwa irin na kasar Sin, da yin iyakacin kokarin samun bunkasuwa mai inganci, da ma kara bude kofa ga waje a nan gaba. Ba shakka, irin wadannan matakai za su baiwa dukkanin fadin duniya, ciki har da kasar Rasha sabbin damamaki na neman samun bunkasuwa.
Sannan a gabannin ziyarar shugaban kasar Sin Xi Jinping a kasar Rasha, takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin, shi ma ya wallafa wani bayani mai taken “Rasha da Sin—-dangantakar abokantaka mai kyakkyawar makoma” a cikin jaridar “People’s Daily” ta kasar Sin a ranar 20 ga watan nan, inda a cikin sa ya gai da jama’ar kasar Sin cikin aminci. Ya kuma bayyana cewa, dangantakar dake tsakanin kasashen Rasha da Sin, wani abin koyi ne na hadin gwiwa cikin jituwa, da kirkire-kirkire a tsakanin manyan kasashe, yana kuma fatan shawarwarin da da zai yi da shugaba Xi Jinping, za su kara sanya sabon kuzari cikin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu daga dukkan fannoni.
Putin ya bayyana a cikin bayanin cewa, ziyarar ta shugaba Xi Jinping tana da babbar ma’ana, wadda ta sake tabbatar da cewa, dangantakar dake tsakanin Rasha da Sin ta kasance ta musamman, kuma a ko da yaushe, ta dogara ne kan amincewa da juna, da mutunta mulkin kai da moriyar juna.
Bayanin ya ce, ko da yaushe kasashen Rasha da Sin, suna dukufa wajen kafa tsarin tsaro na shiyya-shiyya, da na duniya baki daya, wanda zai zama daidai, a bude, kuma ba za a goyi bayan hari kan bangare na uku ba. (Mai fassara: Amina Xu, Saminu Alhassan, Bilkisu Xin)