Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada muhimmancin bude sabon babin aiwatar da dokokin kundin tsarin mulkin kasar a sabon zamani, yayin da a bana kasar ke cika shekaru 40 da fara aiwatar da kundin tsarin mulkin kasar na yanzu.
Cikin wata makala da aka wallafa a Litinin din nan, shugaba Xi ya ce akwai bukatar kara azama wajen wayar da kan al’ummar kasa game da tsarin mulki, da tafiya tare da ruhin tsarin mulki, da yayata matakan aiwatar da tsarin mulki, da kyautata hanyoyin cin gajiyar hakan a fannin jagoranci.
Shugaba Xi ya ce ta hanyar aiwatar da wadannan matakai, ana iya samun tabbaci na gina kasar Sin mai sigar gurguzu ta zamani a dukkanin fannoni, tare da ingiza babbar farfadowar kasar Sin daga dukkanin fannonin ci gaba. (Saminu Alhassan)